Wani abu ya yi bindiga da dalibin Islamiyya a Kaduna
An gano dalibin Islamiyyar ne ya dauko wani abu daga daji wanda ya fashe a cikin makarantar.
Wani abu ya fashe a wata makarantar Islamiyya, inda dalibi daya ya rasu, sannan wasu 10 suka jikkata a kauyen Kidandan da ke Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kaduna.
- NAJERIYA A YAU: Dabaru 10 Na Kaucewa Masu Garkuwa Da Mutane
- An ceto mutumin da ’yan bindiga suka sace a Abuja
Aruwan ya ce, “Rahotannin farko da jami’an tsaro suka gudanar, ya nuna daya daga cikin daliban makarantar ya dauko wani abu daga cikin daji, wanda daga baya ya fashe a cikin makarantar.”
Aruwan, ya ce an tabbatar da mutuwar dalibi daya mai suna Zaidu Usman, yayin da wasu dalibai 10 suka samu rauni.
A cewarsa tuni aka kai wadanda suka ji rauni zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, a Zariya.
“Gwamna Uba Sani ya kadu tare da bakin cikin faruwar lamarin, ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga wadanda abin ya shafa da iyalansu.
“Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikan wanda ya rasu, ya kuma bai wa ragowar da suka jikkata lafiya.”
Ya ce gwamnan ya kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su kara sanya ido kan ‘ya’yansu da unguwanni, ganin yadda wasu yankunan jihar ke fuskantar matsalar tsaro.
Aruwan, ya kuma ce gwamnan ya umarci jami’an tsaro su gudanar da bincike kan lamarin.