Wani Alhaji
Wani danfulani ne ya je Makka ya dawo, sai abokansa suka zo suna yi masa barka da zuwa. To daya daga cikinsu sai ya kira shi da sunansa ba tare ya ce masa Alhaji ba, sai daya daga cikinsu ya ce: “Ba za ka kira shi da Alhaji ba? Sai Alhajin ya ce: “Rabu da […]
Wani danfulani ne ya je Makka ya dawo, sai abokansa suka zo suna yi masa barka da zuwa. To daya daga cikinsu sai ya kira shi da sunansa ba tare ya ce masa Alhaji ba, sai daya daga cikinsu ya ce: “Ba za ka kira shi da Alhaji ba? Sai Alhajin ya ce: “Rabu da shi, rabu da shi, iya alhakin da mala’iku suka rubuta masa ya ishe shi!”
Daga Isma’il Adamu Manzo Kiyawa.