Alhajin Jihar Legas Ya Rasu A Makka

Daya daga cikin mahajjatan Jihar Legas, Alhaji Oloshogbo Isiaka Idris, ya rasu bayan ya dawo daga dawafi a Makkah. Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Legas, Saheed Onipede, ya ce Alhaji Isiaka mai shekaru 68 ya rasu ne a lokacin da yake cin abinci bayan sallar Magriba a ranar Talata. Onipede ya kara da […]

Alhajin Jihar Legas Ya Rasu A Makka

Massalacin Makkah

Daya daga cikin mahajjatan Jihar Legas, Alhaji Oloshogbo Isiaka Idris, ya rasu bayan ya dawo daga dawafi a Makkah.

Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Legas, Saheed Onipede, ya ce Alhaji Isiaka mai shekaru 68 ya rasu ne a lokacin da yake cin abinci bayan sallar Magriba a ranar Talata.

Onipede ya kara da cewa an yi jana’izar marigayin a Makkah kamar yadda addinin musulunci ya shar’anta.

Ya jaddada cewa, yayin da har yanzu ba a kai ga gano musabbabin mutuwar dattijon a  likitance ba, ana hasahsen cewa ya gamu da ajalinsa ne sakamakon wani abu mai nasaba da cutar hawan jini, sanadiyyar  ’yar gajiyar da ya yi  lokacin dawafi.

Saheed Onipede ya mika ta’aziyyar gwamnatin jihar Legas ga iyalai, ’yan uwa da abokan arzikin marigayin wanda ya fito daga Karamar Hukumar Shomolu.

Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya kuma ba shi Aljannah Fridausi da kuma ladan aikin Hajji, tunda ya riga ya yi niyya.

Sakataren hukumar ya yi kira ga sauran alhazai da su yi taka-tsan-tsan, kuma su kula da kansu kafin a fara gudanar da ayyukan Hajji gadan-gadan.

Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin  Musulunci, Dakta Ahmad Abdullahi Jebe, ya bayyana cewa mahajjatan jihar suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kuma yana fatan za su ci gaba da irin wadannan halaye da dabi’u a Makkah inda za a jima ana gudanar da ibada.

Shi ma shugaban hukumar, Imam Injiniya Shakiru Ayinde Gafar, ya yaba wa mahajjatan bisa hakuri da juriya da suka nuna.