Wani babban jami’in gwamnati ya halaka kansa

Wani babban jami’in Gwamnatin Jihar Legas, mai mukamin Darakta a Ma’aikatar Walwalar Matasa, Mista Oludare Buraimoh ya rataye kansa a jikin rufin ɗakinsa, inda ya mutu. Daraktan, wanda ke zaune a rukunin gidaje na Unity da ke unguwar Gbonnagun a Abekuta a Jihar Ogun ya kashe kansa ne da misalin ƙarfe 4 na safiyar Litinin […]

Wani babban jami’in gwamnati ya halaka kansa

Wani babban jami’in Gwamnatin Jihar Legas, mai mukamin Darakta a Ma’aikatar Walwalar Matasa, Mista Oludare Buraimoh ya rataye kansa a jikin rufin ɗakinsa, inda ya mutu.

Daraktan, wanda ke zaune a rukunin gidaje na Unity da ke unguwar Gbonnagun a Abekuta a Jihar Ogun ya kashe kansa ne da misalin ƙarfe 4 na safiyar Litinin da ta gabata, bayan ya shiga ɗakin ɗansa, Dotun wanda ke fama da zazzaɓin malariya inda ya ba shi maganinsa ya ce ya sha. Yaron ya shaida cewa bayan da bai ji muryar mahaifin nasa ba a ɗakin sai ya leƙa domin ya ga abin da ke faruwa, inda ya tarar da gawar mahaifin nasa rataye a jikin rufin dakin, tana lilo; inda nan take ya yi kururuwa maƙwabta suka taru a gidan kafin daga bisa ni a ankarar da ‘yan sanda. Dotun ya ce ya tarar da kujerar da mahaifin nasa ya taka, sannan ya yi amfani da irin zanin saƙar nan na ashoke, ya ɗaure wuyansa a jikin rufin dakin.

A cewar uwargidan mamacin, mijin nata bai nuna wata alamar yana tattare da damuwa ba kafin ya halaka kansa. Ta ce wannan lokaci ne da ya kamata su ji daɗin rayuwarsu, bayan gwagwarmayar da ya sha a rayuwa sai ga shi ya halaka kansa.

’Yan sanda a ofishin Obantoko Abeokuta, inda a nan ne aka shigar da maganar, sun tabbatar da abkuwar lamarin. Tuni dai aka kai gawar mamacin babban asibintin garin Abekuta domin gudanar da bincike.