… Wani Ba’Indiye ma ya shekara 40 bai yi wanka ba

Wani Ba’Indiye, dan shekara 65, mai suna Guru Kallash, ya daina yin wanka tun a shekarar 1974, kimanin shekara 40 da suka gabata. Ya kuma yi hakan ne don limamin addininsu ya tabbatar masa da samun da namiji, matukar ya jajirce da rashin wanka, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Barcroft ya ruwaito.Har yanzu ’ya’yansa […]

… Wani Ba’Indiye ma ya shekara 40 bai yi wanka ba

Wani Ba’Indiye, dan shekara 65, mai suna Guru Kallash, ya daina yin wanka tun a shekarar 1974, kimanin shekara 40 da suka gabata. Ya kuma yi hakan ne don limamin addininsu ya tabbatar masa da samun da namiji, matukar ya jajirce da rashin wanka, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Barcroft ya ruwaito.
Har yanzu ’ya’yansa mata ne, su bakwai, kuma yana sauraren samun da namiji. A kowace safiya idan ya tashi, Kalalsh kan yi wankan wuta, sannan yana zukar tabar wiwi, a lokacin da yake addu’ar roko abin bautar Hindu Shiba, sannan ya rika yin rawa yana kewaya wuta.
Iyalan Kallash sun taba yin yunkurin tura shi cikin kogi, amma kokarinsu ya ci tura. “Mun sha yin kokarin yi masa wanka, amma al’amarin ya gagara,” a cewar matarsa Kalabati Debi, ’yar shekara 60.
Makwaftan Kallash na nuna masa kyara saboda warin jikinsa