Wani barawo a Amurka ya hadiyye sarkokin wuya da ya sata

Wani barawo da aka tuhume shi da haura gidan mutane, ya hadiyye sakokin mata biyu, inda aka dauki hoton cikinsa kafin aka kai shi kurkuku. Jami’an ’yan sanda sun bayyana cewa kumburin da aka gani a cikinsa ta tabbata sarkokin da ya sato ne, tun a ranar 10 ga Disambar bana.Mutumin mai suna Joseph ramos, […]

Wani barawo a Amurka ya hadiyye sarkokin wuya da ya sata
Wani barawo a Amurka ya hadiyye sarkokin wuya da ya sata

Wani barawo da aka tuhume shi da haura gidan mutane, ya hadiyye sakokin mata biyu, inda aka dauki hoton cikinsa kafin aka kai shi kurkuku. Jami’an ’yan sanda sun bayyana cewa kumburin da aka gani a cikinsa ta tabbata sarkokin da ya sato ne, tun a ranar 10 ga Disambar bana.
Mutumin mai suna Joseph ramos, dan shekara 21, an kama shi ne a ranar 11 ga Disamba, a daidia lokacin da aka tsayar da shi yana tuka motar da ya sato. An samu dimbin kayayyaki a cikin motar.
Lokacin da zda a kai Ramos gidan yari, sai aka dora a kan na’urar daukar hoto ta jami’an tsaro, wadda a Turancin Ingilishi ake kira da  “SecurPass d-ray” nan da nanan na’urar ta bayyana kullin wani bakin abu, da aka yi nazarinsa, sai aka gano cewa a she sakokin wuya ne da ya sato.
Jami’an kula da gidan yari, sun saba yin amfani da na’urar daukar hotonb sassana jikin mutum, tun watan Yunin bana, inda suke gano abubuwan da masu laifin da za a tsare suka boye.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan