Wani barawo da ya shiga gida sata ya buge da girka wa kansa kalaci

Wani barawo da ya shiga wani gida a Florida ta kasar Amurka a farkon makon nan ya buge da girka wa kansa kalaci a gidan a maimakon ya yi satar da ta kai shi gidan ya fice. A lokacin da masu gidan suka farga cewa sun yi mugun bako sai kawai ya fada masu cewa […]

Wani barawo da ya shiga gida sata ya buge da girka wa kansa kalaci

Wani barawo da ya shiga wani gida a Florida ta kasar Amurka a farkon makon nan ya buge da girka wa kansa kalaci a gidan a maimakon ya yi satar da ta kai shi gidan ya fice.

A lokacin da masu gidan suka farga cewa sun yi mugun bako sai kawai ya fada masu cewa “kowa ya koma ya ci gaba da barci.”

Barawon mai suna Gabin Crim ya ci gaba da sha’aninsa a tsanake a cikin gidan da yake da tazarar mil 15 daga Tampa Bay har wajen karfe hudu na asuba lokacin da ’yan sandan Pinellas County suka zo suka kama shi a bayan gida bayan masu gidan sun kira lambar wayar neman agaji ta 911.

Crim mai shekara 19 wanda tsohon sojan ruwa ne binciken ’yan sanda ya nuna cewa yana buge da giya ne lokacin da ya aikata wannan aika-aika.