Wani barawon waya zai ci sarka ta shekara 3 a Legas

Damfara ta jefa barawon cikin tsaka mai wuya.

Wani barawon waya zai ci sarka ta shekara 3 a Legas

Wata kotu a Jihar Legas ta yanke wa wani barawo hukunci cin sarka na shekara uku a gidan kaso bayan samunsa da laifin satar wayar hannu da kudi da suka kai Naira 450,000.

A ranar Juma’a ce Kotun ta Majistire da ke zamanta a Ikeja, ta yanke wa barawon hukuncin kari a kan tarar kudi ta Naira 150,000 da yanka masa.

Alkalin kotun, Mista L. A. Owolabi, ya ce dole ne barawon ya biya adadin kudaden da ya sata tare da biyan kudin wayar da ya dauke kafin fara biyan tarar da aka shata masa.

Owolabi, ya jadadda cewar hukunci zai zama izina ga masu aikata laifi irin nasa.

Tun da farko mai gabatar da kara, Innocent Odugbo, ya bayyana wa kotun cewar barawon ya aikata laifin a ranar 19 ga watan Janairun 2021 a yankin Oshodi na Jihar Legas.

A cewarsa, “barawon ya hada baki da wasu mutane suka damfari wata mata mai suna Precious Asibezim wayarta da ta kai darajar kudi N200,000.

“Sannan suka mata dabara ta tura musu kudi har N450,000 zuwa wani asusun ajiyar banki.

“Bayan matar ta gano sun yi mata ‘sibaran na bayye’ suka yi mata sai ta sanar da ‘yan sanda abin da ya faru.

Aminiya ta ruwaito cewa, ragowar mutanen da suka aikata laifin sun tsere yayin da shi kuma dayan ya shiga hannun jami’an tsaro.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno