Wani Bishop dan luwadi zai saki mijinsa
Wani Bishop mai suna Gene Robinson, limanmin cocin na farko a tarihi da ya taba bayyana kansa a matsayin dan luwadi, ya ce zai saki mijinsa Mark Andrew wanda suka shafe kimanin shekara 25 a tare.Bishop din na wata cocin Anglikan da ke Amurka ya bayyana wa kafar yada labarai ta Daily Beast cewa, “ya […]
Wani Bishop mai suna Gene Robinson, limanmin cocin na farko a tarihi da ya taba bayyana kansa a matsayin dan luwadi, ya ce zai saki mijinsa Mark Andrew wanda suka shafe kimanin shekara 25 a tare.
Bishop din na wata cocin Anglikan da ke Amurka ya bayyana wa kafar yada labarai ta Daily Beast cewa, “ya gode wa abokin zamansa” kumasabanin da yayi sanadiyyar mutuwar auransu wanda aka daura a shekarar 2003, bai shafi kowa ba. Sai dai tun lokacin da aka daura aurar, mabiyan cocin suka rabu gida biyu inda wasu kai Allah-wadai da shi, wasu daga ciki kuma suka balle daga cocinsa.
Mista Gene wandajigo ne a fafutukaraurar jinsi daya, ya bayyana a wata wasika da ya rubuta cewa: “Ba na jin dadin yadda ake gallaza wa ‘yan luwadi da madigo a fadin duniya don kawai sun zabi abin da ransu yake so.” Injishi
Bishop danshekara 66 ya taba aurar wata mata inda suka samu ‘ya’ya biyu da ita. Amma sun rabu da itatun a shekarar 1985 dalili da dabi’unsa na ‘yan luwadi.