Wani dan acaba ya bace a Kafanchan
Wani matashi mai sana’ar acaba a garin Kafanchan, Jihar Kaduna, dan kimanin shekara 23 da haihuwa mai suna Salisu, wanda aka fi sani da ‘Kwakuleto’ ya bace, ba a san inda yake ba, tun bayan da ya fita aiki kwana 17 da suka gabata. Kamar yadda Aminiya ta kalato, Salisu ya kasance yana karbar babur […]

Wani matashi mai sana’ar acaba a garin Kafanchan, Jihar Kaduna, dan kimanin shekara 23 da haihuwa mai suna Salisu, wanda aka fi sani da ‘Kwakuleto’ ya bace, ba a san inda yake ba, tun bayan da ya fita aiki kwana 17 da suka gabata.
Kamar yadda Aminiya ta kalato, Salisu ya kasance yana karbar babur ne don yin aiki idan ya dawo makaranta da rana har zuwa dare kafin wannan lamarin ya faru da shi.
Usama Labaran shi ne mai babur din da Salisu ke yin aiki da shi. Ya bayyana wa Aminiya cewa kusan wata guda ke nan da fara ba shi babur yana aiki da shi. “Da ma ni ina tashi aiki ne da misalin karfe daya na rana, shi kuma sai ya zo da misalin daya da rabi zuwa karfe biyu ya karbi babur din ya yi aiki zuwa karfe takwas ko tara na dare. A ranar da abin zai faru, ya zo ya karbi mashin din da rana shiru-shiru lokacin dawowarsa ya yi ba mu ga ya dawo ba. Na kira wanda suke kwana tare ya ce mani ai bai dawo ba, har zuwa sha biyu na dare bai dawo ba kuma idan mun kira lambarsa ba ta shiga. Tun daga nan hankalinmu ya tashi, ni dai a wannan daren ban yi barci ba,” inji Usama.
Ya ci gaba da cewa, bayan gari ya waye ne suka garzaya ofishin ’yan sanda guda uku da ke Kafanchan amma babu wani labari. “Daga nan muka ci gaba da zagayawa ofisoshin ’yan sanda na garuruwan makwabta da asibitoci daban-daban ko za a samu wani labari amma ba duka shiru. Mu dai yanzu ba mu san abin da ya faru da shi ba, sai dai fatanmu Allah Ya bayyana mana halin da yake ciki don hankalinmu ya kwanta.”
Malam Ubale mai Sitika, wanda shi ne marikin Salisu Kwakuleto, ya bayyana wa Aminiya cewa yaron yana shirin ma ya bar aikin mashin ne, domin kafin faruwar abin da ya faru da shi ma har ya kama hayar shago ya sayi firiji don zuba kayan zaki da kuma cajin waya. “A yanzu fatanmu shi ne Allah Ya bayyana mana halin da yake ciki ko yana raye ne ko ba rai, domin washegarin faruwar lamarin mun kai maganar hedkwatar ’yan sanda da na ’yan bijilanti na Kafanchan.”