Wani dan banga ya gurfana gaban kotu kan cin zarafi
Wani dan banga a garin Gombe mai suna Bala danbanga ya gurfana a gaban kotu bisa zargin cin zarafin wasu mutum biyu.Mutanen wa da kane masu suna Abubakar Muhammad da Umar Muhammad da suke zaune a Unguwar Kagarawal sun yi karar Bala danbanga ne da ke zaune a Unguwar Sabon Fegin Malam Inna, gaban Kotun […]
Wani dan banga a garin Gombe mai suna Bala danbanga ya gurfana a gaban kotu bisa zargin cin zarafin wasu mutum biyu.
Mutanen wa da kane masu suna Abubakar Muhammad da Umar Muhammad da suke zaune a Unguwar Kagarawal sun yi karar Bala danbanga ne da ke zaune a Unguwar Sabon Fegin Malam Inna, gaban Kotun Yanki ta Jeka-Da-Fari inda Mai shari’a Bashiru Abubakar Bappah ke alkalanci suna kukan dan bangar ya yi ta yi dukan Umar da bulalar kebur, ba tare da laifin komai ba sai saboda ya je neman makwabcin Umar din bai same shi ba.
Sun ce Bala danbanga ya bulali Umar din ne don ya ce masa bai san inda wanda yake nema yake ba, inda bayan ya koma ofishinsu na banga sai ya taho da wasu ’yan banga suka tafi da Umar ofishinsu suka yi ta dukansa har ya suma.
Sun ce bayan Umar ya suma sai Bala danbanga ya daure hannuwansa biyu da ankwa suka kai shi gidansa suka bincike gidan da iyalansa ba tare da izinin hukuma ba, inda kotun ta ce aikata hakan laifi ne a karkashin sassa na 262 da 264 na kundin laifuffuka da hukuncinsu (Penal Code).
Da kotun ta waiwayi Bala danbanga ya amince da laifinsa bisa cewa suna aiki ne da ofishin ’yan sanda na Gombe, kuma su ne suka ce musu su rika dukan mutane suna daure su.
Alkalin kotun Mai shari’a Bashiru Bappah ya ba da belinsa bisa sharadin wanda zai tsaa masa ya kasance shugaban kungiyar ’yan banga na Gombe kuma sai ya fadi dokar da ta kafa su kan rika aikata hakan. Kuma sai ya mallaki gida a fadar jihar kuma ya kasance mazaunin garin Gombe tare da ba da cikakken direshinsa da kananan hotunansa biyu da lambar wayarsa.
Da aka rasa wanda zai cika wadannan ka’idojin, sai kotun ta yi amfani da kashi na 183 na kundin manyan laifuffuka ta tura dan bangar gidan kurkuku zuwa yau Juma’a don ci gaba da sauraron karar.