Wani dan Iran ya shekara 60 bai yi wanka ba

Wani mutumin kasar Iran ya kafa tarihi, inda ya shafe shekara 60 ba tare da yin wanka ba, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na kasar IRNA, ya ruwaito labarin mutumin dan shekara 80.A rahoton an bayyana cewa, mutumin mai suna Amoo Hadj, yana zaune ne a kauyen Dezhgah da ke Dehram a gundumar Fars da […]

Wani dan Iran ya shekara 60 bai yi wanka ba

Wani mutumin kasar Iran ya kafa tarihi, inda ya shafe shekara 60 ba tare da yin wanka ba, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na kasar IRNA, ya ruwaito labarin mutumin dan shekara 80.
A rahoton an bayyana cewa, mutumin mai suna Amoo Hadj, yana zaune ne a kauyen Dezhgah da ke Dehram a gundumar Fars da ke kasar Iran. Mutumin na cin mushe, kuma yana shan tabar bututu, mai tsawon inci uku; kuma garin tabar da ake dura mata, shi ne busasshen kashin dabbobi. Amoo Hadj yana zaune ne a cikin wani dan daki da aka gina da dutse, a cikin wani rami, tamkar kabari.
Kamfanin Dillancin Labaran, ya bayyana cewa, a duk lokacin da muttumin yake jin sanyi, sai ya sanya hular kwano, sannan y

Amoo Hadj, Ba’Iraniyen da ya shekara 60 ba wanka

a yi ta kunna taba yana zuka