Wani dan jarida ya rasu yana cikin rubuta rahoto
A ranar alhamis din makon jiya ne Allah ya yi wa wani dan jarida mai suna Ibrahim Aliyu da ke aiki a sashin watsa labarai na Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi (Sa’adu Zungur Press Center) rasuwa a daidai lokacin da yake rubuta wani rahoto. Ibrahim Aliyu wanda shi ne wakilin gidan talabijin na jihr (BATb) ya […]
A ranar alhamis din makon jiya ne Allah ya yi wa wani dan jarida mai suna Ibrahim Aliyu da ke aiki a sashin watsa labarai na Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi (Sa’adu Zungur Press Center) rasuwa a daidai lokacin da yake rubuta wani rahoto.
Ibrahim Aliyu wanda shi ne wakilin gidan talabijin na jihr (BATb) ya shafe sama da shekara takwas yana aiki a gidan gwamnatin.
Da yake zantawa da wakilinmu Daraktan Watsa Labarai na Gidan Gwamnatin Alhaji Ibrahim Sani ya ce marigayin mutumin kirki ne mai gaskiya da rikon amana.
Ya kara da cewa marigayin kwararren dan jarida ne da za a dauki lokaci mai tsawo ana tunawa da gudunmawar da ya bayar wajen ciyar da Jihar Bauchi gaba.
Alhaji Ibrahim Sani ya kara da cewa marigayin ya kawo sauyi a sashin watsa labarai na gidan gwamnati kuma Gwamna Isa Yuguda ya nuna alhininsa da rasuwar marigayin. Kuma daga bisani Gwamna Yuguda ya ziyarci gidan marigayin da ke Unguwar Bakaro a garin Bauchi domin yin ta’aziyya ga iyalansa.
Marigayin ya rasu yana da shekara 39 kuma ya bar mata biyu da ’ya’ya shida.