Wani dan kasar Sin ya yi karar hukuma kan gazawar shawo kan hazo

Wani mutumin kasar Sin da ke zaune a Arewacin birnin Shijiazhuang, babban birnin gundumar Hebei, ya gabatar wa kotun yanki korafi, inda ya bukaci ta tursasa Hukumar Kula da Muhallai ta birnin Shijiazhuang ta “yi aiki tukuru wajen shawo kan gurbacewar iskar muhalli, kamar yadda doka ta tanada,” kamar yadda jaridar Yanzhao Metropolis Daily ta […]

Wani dan kasar Sin ya yi karar hukuma kan gazawar shawo kan hazo

Wani mutumin kasar Sin da ke zaune a Arewacin birnin Shijiazhuang, babban birnin gundumar Hebei, ya gabatar wa kotun yanki korafi, inda ya bukaci ta tursasa Hukumar Kula da Muhallai ta birnin Shijiazhuang ta “yi aiki tukuru wajen shawo kan gurbacewar iskar muhalli, kamar yadda doka ta tanada,” kamar yadda jaridar Yanzhao Metropolis Daily ta ruwaito.
Mutumin mai suna Mista Li Guidin, ya bukaci hukumar kula da muhallin ta ba shi diyya, kan hazon da ya baibaye birhnin Shijiazhuang, tare da daukacin Arewacin kasar Sin a lokacin hunturu.
Mista Li, shi ne mutumin farko da ya fara kai hukuma kara, kan matsalar hazo, don haka har yanzu daidai ba tantance ba, kan ko kotu za ta amince da karar Mista Li.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan