Wani dan Kuwait ya nuna wa Limami bindiga don ya hana shi tara kudin taimako a Masallaci

Yan sanda sun kama wani mutum da ya nuna wa limami bindiga a masallaci, bayan da ya hana shi tara wa mutanen Siriya kudi a kasar Kuwait. Wanda ake zargi dan kasar Kuwait, ya kwace kakakin magana, bayan an kammala sallar Juma’a, inda ya roki masu ibada da suka tara kudin gudunmuwa don taimaka wa […]

Wani dan Kuwait ya nuna wa Limami bindiga don ya hana shi tara kudin taimako a Masallaci
Wani dan Kuwait ya nuna wa Limami bindiga don ya hana shi tara kudin taimako a Masallaci

Yan sanda sun kama wani mutum da ya nuna wa limami bindiga a masallaci, bayan da ya hana shi tara wa mutanen Siriya kudi a kasar Kuwait. Wanda ake zargi dan kasar Kuwait, ya kwace kakakin magana, bayan an kammala sallar Juma’a, inda ya roki masu ibada da suka tara kudin gudunmuwa don taimaka wa al’ummar kasar Siriya.
Shi kuwa limamin masallacin, sai ya sake fizge kakakin maganar daga hannunsa, inda ya bayyana wa mutane cewa ‘wannan mutumin ba shi da ikon yin wannan kira na tara kudi. Ya kuma ce akwai kwamitoci da aka kafa don tara kudin tallafink, kamar yadda jaridar Al Watan da ake buga cikin harshen Larabci ta ruwaito.
Jin sukar da Liman ya yi wa kalaman wannan mutmin, wanda ba a ambaci sunansa ba, sai ya dage kan lallai sai ya yi wa jama’a jawabi a masallaci, hart a kai ga ya dauko bindiga ya nunata a fuskar limamin. Nan take masallata suka yunkura don ceton limaminsu. Shi kuwa mai bindiga sai ya tsere. Jaridar ta ruwaito cewa daga nan ya saci motar wani bako da ke aiki a kasar, inda ya riga harbin ’yan sandan da ke binsa. Da ’yan sanda suka samu umarnin mayar da martani, sai suka bude masa wuta, har suka samu suka kama shi, a daidai lokacin da yake yunkurin shiga cikin sahara ya bace. Bincike dai ya nuna mutumin ma’aikacin ma’aikatar tara kudin taimakon al’umma ne a kasar, kuma ya mallaki bindigogi biyu; sannan yana cikin jerin masu laifin da ’yan sanda ke nema a kasar.
kasar Kuwait da sauran kasashen yankin Tekun Fasha sun hana tara kudin tallafi ga al’umamr Siriya, sai dai akwai kungiyoyi masu lasisi da aka ba su izini tara agajin, don haka su ke karbar taimako a kasar.