Wani dan sanda da ya yi wa yarinya fyade a Kano
Ana tuhumar wani dan sanda mai suna Jonathan Gana da yi wa wata yarinya fyade, inda aka yi zargin cewa a ranar Lahadi 19 ga Mayun da ya gabata ya yi wa yarinyar mai kimanin shekara 14 fyade a Unguwar Fanshekara a karamar Hukumar Kunbotso, Jihar Kano, ta hanyar yi mata barazana da bindiga.Yarinyar mai […]
Ana tuhumar wani dan sanda mai suna Jonathan Gana da yi wa wata yarinya fyade, inda aka yi zargin cewa a ranar Lahadi 19 ga Mayun da ya gabata ya yi wa yarinyar mai kimanin shekara 14 fyade a Unguwar Fanshekara a karamar Hukumar Kunbotso, Jihar Kano, ta hanyar yi mata barazana da bindiga.
Yarinyar mai suna Fatima dahiru (ba sunan gaskiya ba) ta shaida wa Aminiya cewa “Bayan Sallar Magariba zan kai wa yayana kayan askinsa (clipper) na kunna fitilar wayar matarsa don na ga haske, sai na ji mun yi karo da dan sandan. Na tsaya na ba shi hakuri, amma sai ya nuna min bindiga cewa tunda na bangaje shi sai ya kai ni barikinsu an daure ni shekara takwas.”
Ta ce ta ci gaba da ba shi hakuri, amma ya ki suna tafe tana ba shi hakuri har suka kai filin wata makarantar sakandare sai ya ce ta tsaya. “Ya tambaya ina da saurayi sai na ce a’a. Na san namiji? Na ce ni babana da yayana kawai na sani. Sai ya ce yau zan san namiji. Sai ya ce na shiga cikin wani babban bututun ruwa da ke wurin. Na ki shiga ina kuka ina ba shi hakuri, sai ya dauko bindiga ya ce zai harbe ni idan ban shiga ba. Sai na shige ciki, ya kwance jakarsa da ke goye a bayansa ya ce na yi matashin kai da ita. Sannan ya shigo ciki rike da bindiga ya yi lalata da ni. Da ya gama, sai ya ce na tafi gida. Kuma ya yi min kashedi cewa idan ya gan ni a hanya ya nemi na zo na ki, to, zai murza wasu zobba da ke hannunsa da ya ce na asiri ne, kuma daga nan zan zama ruwa na bi iska ba zan sake komawa mutum ba,” inji ta.
Ta ce da yayanta ya bugo waya yana tambayarta yaya ya ji shiru ba ta kai masa aikensa ba, sai ta kasa ba shi amsa sai kuka kawai take yi. “Jin haka sai yake tambayata me ya faru, na gaya masa. Nan da nan ya zo shi da abokinsa suka same ni, inda na raka su wurin da abin ya faru, kuma muka iske dan sandan a wurin,” inji ta.
Yayanta Malam Auwalu Salisu ya tabbatar da bayanan da ta yi, inda ya ce da ta raka su wurin, “Sai muka yi sa’a dan sandan na wurin bai je ko’ina ba. Sai na kira mahaifinmu a waya na sanar da shi, ya yi sauri ya same mu a wurin. Da muka tambayi dan sandan abin da ke tsakaninsa da ita sai ya ce wai taka shi ta yi. Sai muka ce maganar fyade muke son ji. Da muka ga yana yi mana hanya-hanya sai muka nemi ya zo mu je ofishin ’yan sanda, shi kuma ya dage sai dai mu je command din su. Muna cikin jayayya ne mutane suka taru, inda matasan unguwa suka nemi su yi masa duka, amma dattijan unguwa suka shiga tsakani. Sannan muka hadu gaba daya muka tafi ofishin ’yan sanda na Fanshekara,” inji shi.
Ya ce DPO ya ba da umarnin a je gwaji a asibiti, inda sakamako ya nuna dan sandan ya yi amfani da ita, sai DPO ya dauki alwashin tsare shi, ya sallame su zuwa kwana biyu. “Da muka koma sai aka kai mu Bompai. Mun je Bompai sau uku, sai aka ce mu daina zuwa sai an tuntube mu. Sai ranar Litinin 17 ga Yuni muka je aka hada mu da dan sandan aka yi mana tambayoyi aka sallame mu ba tare da an yi wa Jonathan tambaya ko daya a gabanmu ba,” inji shi.
Ya ce jan kafar da ake yi kan lamarin a ofishin na Bompai, ya sa suke da shakku kan za samu adalci.
Dattijan Unguwar Fanshekara da Malam Umar Sadik ya wakilta sun roki Mai martaba Sarkin Kano da Kwamishinan ‘Yan sanda da Gwamnan Kano su taimaka su nema wa iyalan yarinyar hakkinsu ta hanyar tabbatar da adalci.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano Magaji Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce dan sandan ya amsa laifinsa kuma da zarar an kammala zaman shari’a a matakin ’yan sanda za a yanke masa hukuncin da ya dace.