Wani dattijo ya kashe wata budurwa a Ghana

A ranar Asabar da ta gabata ne wani malamin makarantar boko mai kimanin shekara 70 ya kashe wata budurwa  ’yar shekara 16 a gidansa da ke garin Aboaso da ke kusa da Jihar Ashanti a kasar Ghana, inda sakamakon wannan kisan garin ya fada cikin rudani.Rohotanni sun ruwaito cewa mutumin mai suna Ben Addai dai […]

Wani dattijo ya kashe wata budurwa a Ghana
Wani dattijo ya kashe wata budurwa a Ghana

A ranar Asabar da ta gabata ne wani malamin makarantar boko mai kimanin shekara 70 ya kashe wata budurwa  ’yar shekara 16 a gidansa da ke garin Aboaso da ke kusa da Jihar Ashanti a kasar Ghana, inda sakamakon wannan kisan garin ya fada cikin rudani.
Rohotanni sun ruwaito cewa mutumin mai suna Ben Addai dai ya kashe budurwar ce bayan ya yi lalata da ita. Kuma an bayyana sunan yarinyar da Asante Juapong wadda  take shekara ta biyu ne a makarantar sakandare.
‘’Bayan  ya gama lalata da ita sai ya soke ta da wuka ya arce, amma an yi sa’ar gano shi a wata unguwa da ke kusa.” A cewar wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta.
Wasu shaidu sun bayyana cewa budurwar ta sha gaya musu cewa “mutumin na damunta da bukatar yayi lalata da ita.Haka kuma sun sha ganin budurwan na hira da mutumin a wajen gidansa, sai dai da sanyin safiyar ranar Asabar sun ga budurwan ta rugo a guje daga dakin dattijon tsirara cikin jini kana hanjin cikin a waje. Mun kai mata agaji, inda muka ruga da ita asbitin koyarwa na Komfo Anokye da ke birnin Kumasi,  inda daga baya bisani aka bayyana cewa ta rasu.”
Da wakilinmu  ya tuntubi jamí’an ’yan sandan yankin sun tabbatar da faruwar lamarin. Kuma sun ce mutumin da ake zargi ya shiga hannu, inda suke ci gaba da bincike.