Wani jigo a PDP ya bi sahun Obasanjo ya yaga katinsa
Wani jigo a Jam’iyyar PDP kuma Mashawarcin Gwamnan Jihar Gombe kan Harkokin Tsaro Alhaji Abdullahi Babangida Muhammad ya bi sahun Cif Obasanjo inda yak eta katinsa na zama dan jam’iyyar.Alhaji Abdullahi Babangida Muhammad, ya bayyana wa Aminiya cewa ya fice daga Jam’iyyar PDP ya koma APC, inda ya ce ya ajiye mukaminsa na mai taimaka […]
Wani jigo a Jam’iyyar PDP kuma Mashawarcin Gwamnan Jihar Gombe kan
Harkokin Tsaro Alhaji Abdullahi Babangida Muhammad ya bi sahun Cif Obasanjo inda yak eta katinsa na zama dan jam’iyyar.
Alhaji Abdullahi Babangida Muhammad, ya bayyana wa Aminiya cewa ya fice daga Jam’iyyar PDP ya koma APC, inda ya ce ya ajiye mukaminsa na mai taimaka wa Gwamnan ne ya kuma fice daga PDP har yaga katin zama dan jam’iyyar saboda ba a daukar shawarwarinsa kuma ya ce babu dimokuradiyya a PDP.
Ya ce a matsayinsa na mai taimaka wa Gwamnan a baya yana rike da mukamin ne kawai a matsayin suna amma duk da kasancewarsa masanin harkar tsaro ko ya rubuta matsalar da ke akwai, a boye ko a fili ba a dauka kuma dukkan hadiman Gwamnan ba a amfani da shawararsu.
Alhaji Abdullahi Babangida ya ce wadanda ake yarda da shawarwarinsu a fannin tsaro dukkansu babu wanda yake da horo ko na dan sikawut.
Alhaji Abdullahi, ya ce a matsayinsa na Sakataren Kwamitin Kula da Tsaro na Jihar yakan rubuta wa Gwamna tsare-tsaren aikinsu da duk abin da za a zartar kan tsaro amma ba a amfani da shi, kuma ko a Majalisar Tsaro ta Jihar ba a zama da su.
“Rashin amfani da shawarwarinmu kan tsaro ya jawo tabarbarewar tsaro a jihar, a kasar ma rashin karbar shawarwari daga masana ya sa aka fada wannan hali ga kama-karya irin na PDP da kauce wa bin tsarin dimokuradiyya,” inji Babangida.
Ya ce shekara uku ke nan suna bai wa Gwamnan shawara kan yadda za a yi amma bai dauka, don haka bai zame dole sai sun zauna da shi ko jam’iyyarsa ba, kuma hakan ya sa ya fice daga PDP ya yaga katin zama dan jam’iyyar inda ya bi sahun Cif Obasanjo.
Ya ce muddin jama’a na neman mafita daga halin tabarbarewar tsaro, to su bar PDP su koma APC domin ita ce jam’iyyar da take bin tsarin dokar kasa ba take hakkin kowa ba.
Alhaji Abdullahi, ya ce barazanar da ’yan ta’adda suka yi ta cewa kada a fito zabe, kada jama’a su biye mata. Ya ce ko za a kashe su dole sai sun fito sun yi zabe kuma sai sun karya PDP sun kawo canji mai dorewa a Jihar Gombe da kasar nan.