Wani jigon ’yan Arewa da ke PDP ya koma APC a Jihar oyo

Wani jigo a Jam’iyar PDP bangaren ‘yan Arewa a Jihar Oyo, Sarkin Kudun Yamma, Tafidan Ibadan, Alhaji Hassan Isiyaka, ya canja sheka tare da daruruwan magoya bayansa maza da mata zuwa jam’iyar APC da ke mulki a jihar. A daidai lokacin da wannan labari ya isa kunnen Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya hanzarta […]

Wani jigon ’yan Arewa da ke PDP ya koma APC a Jihar oyo
Wani jigon ’yan Arewa da ke PDP ya koma APC a Jihar oyo

Wani jigo a Jam’iyar PDP bangaren ‘yan Arewa a Jihar Oyo, Sarkin Kudun Yamma, Tafidan Ibadan, Alhaji Hassan Isiyaka, ya canja sheka tare da daruruwan magoya bayansa maza da mata zuwa jam’iyar APC da ke mulki a jihar. A daidai lokacin da wannan labari ya isa kunnen Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya hanzarta gayyatar Alhaji Hassan Isiyaka, zuwa ofishinsa a Ibadan a inda ya yi wata ganawar sirri da shi a karshen makon jiya.

Kafin ya fice daga PDP, Alhaji Hassan Isiyaka da ake yi wa lakabi da Omo-Oba, yana daga cikin fitattun ‘yan siyasa da suka yi gwagwarmayar kafa mulkin PDP a Jihar Oyo, wanda tsohon Gwamnan Jihar, Adebayo Alao Akala, ya ja shi a jiki a zamanin mulkinsa. A bara ne Alhaji Hassan ya jagoranci wasu ‘yan siyasa da suka yi ta manna hotunan Gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa a kan manyan hanyoyi na garuruwan sashen Kudu maso Yamma, domin nuna sha’awarsu ga zabarsa a matsayin Shugaba kasar Najeriya a zaben badi.
Alhaji Hassan Isiyaka yana tare ne da Jagoran ‘yan Arewa magoya bayan APC a Jihar Oyo, Alhaji Yahya Dauda, a lokacin ganawar da Gwamna Abiola Ajimobi ya yi da su, wacce ba a kyale ‘yan jarida sun shiga cikin zauren taron ba.
Bayan ganawar, wakilinmu ya zanta da wannan jigo wanda ya ce, da shi da dimbin magoya bayansa sun yanke shawarar kaurace wa PDP zuwa APC ne a dalilin irin abin da ya kira wasan yara da shugabannin PDP suka dade suna yi a tsakanin su ya-su a Jihar Oyo.
“Shugabannin PDP sun dade suna kai ruwa rana da suka kasa shawo kan matsalar da ke tsakaninsu, wacce ita ce ta taimaka wajen kasa cin zaben shekara ta 2011. Yanzu kuma, wani gungu na fitattun ‘yan asalin Ibadan su bakwai da suke samun goyon bayan wasu masu fada aji sun fito kowannensu yana son tsayawa takarar kujerar Gwamna a zaben shekarar2015 da suke ikirarin cewa, lallai ne a tsayar da daya daga cikinsu a matsayin dan takarar gwamna a zabe mai gabatowa. Wannan ne ya kara rikirkita al’amari da muka yanke shawarar kaurace musu, saboda karan-tsaye da suke yi wa tsarin dimokuradiyya. Sannan kuma shugabannin PDP na kasa sun kara dagula al’amarin jam’iyar baki daya ta fannin dagewar da suka yi a kan Shugaba Goodluck Jonathan, kadai ne dan takarar shugabancin kasa a zaben mai gabatowa. Ai wannan ya saba wa tsarin mulkin dimokuradiyya, har kai gab a samu nasara ba,” inji shi.
Dangane da tattaunawar da suka yi da Gwamnan, sai Alhaji Hassan Omo-Oba, ya ce, “Gwamna Ajimobi, ya nuna mana jin dadinsa ne a kan wannan batu na canja shekar da muka yi, kuma ya tabbatar mana da samun guraben ayyuka da mukamai, domin tsoma mu cikin mulkinsa. Sannan, mun tattauna a kan ranar da za a tsayar domin yin bikin karbarmu cikin APC a Jihar Oyo.”