Wani jirgin sama ya fadi a Jihar Kebbi
Wani jirgin sama mai lamba 5NBG2 na kamfanin Westlink Airlines mai daukar mutum shida ya fadi da mutum biyu a garin Matseri a karamar Hukumar Bunza a Jihar Kebbi. Sarkin Kudun Matseri Alhaji Muhammad Bello Ahmed da hadarin ya auku a kusa da garinsa, ya bayyana wa aminiya cewa jirgin ya fadi ne bayan ya […]
Wani jirgin sama mai lamba 5NBG2 na kamfanin Westlink Airlines mai daukar mutum shida ya fadi da mutum biyu a garin Matseri a karamar Hukumar Bunza a Jihar Kebbi.
Sarkin Kudun Matseri Alhaji Muhammad Bello Ahmed da hadarin ya auku a kusa da garinsa, ya bayyana wa aminiya cewa jirgin ya fadi ne bayan ya tsinke wayar wutar lantarkin Matseri. Ya ce, bayan jirgin ya fadi sun isa wurin shi da jama’arsa sun samu mutun guda da ya yi amfani da lema ya sauko kafin jirgin ya fadi, kuma cikinsu ba wanda ya rasu.
Sarkin ya ce mutanen sun shaida masa cewa daga Ma’aikatar Gona ta Tarayya aka turo su zuwa Zamfara da Sakkwato da Kebbi domin su yi feshin maganin kwari da tsuntsaye, kuma sun onakin sun gama da Zamfara da Sakkwato za su fara da Jihar Kebbi ne lamarin ya faru.
Sun bayyana sunansu da Solomon Mshelia da Ibrahim da bai fadi sunansa na biyu ba, kuma Sarkin ya mika su ga babban jami’in ’yan sandan Bunza.
Sarkin ya ce a gaskiya karamar hukuma ko fadar Sarkin Gwandu ba wanda ya shaida musu za a zo feshi yankinsu, kuma koda jirgin ya fadi ba su ga kayan feshi ko maganin feshi a cikinsa ba.
Rundunar ’Yan sanda Jihar Kebbi ta bakin Kakakinta ASP Kabiru Bawa Rawayau ta tabbata wa Aminiya da aukuwar hadarin.