Wani kamfani ya kaddamar da sabon magani
Kamfanin magunguna mai suna BF SUMA ya kaddamar da sabon maganinsa wanda yake taimaka wa jiki tace kayan abinci cikin sauki. Kamfanin ya kaddamar da sabon maganin a bikin karshen shekara da kamfanin ya shirya, a karshen makon da ya gabata, Abuja. Babban Manajan Kamfanin na Najeriya, Leo Wei, ya ce kamfanin ya bullo da […]
Kamfanin magunguna mai suna BF SUMA ya kaddamar da sabon maganinsa wanda yake taimaka wa jiki tace kayan abinci cikin sauki.
Kamfanin ya kaddamar da sabon maganin a bikin karshen shekara da kamfanin ya shirya, a karshen makon da ya gabata, Abuja.
Babban Manajan Kamfanin na Najeriya, Leo Wei, ya ce kamfanin ya bullo da maganin ne don ya taimaka wa al’umma su samu abinci mai kyau a jikinsu.
“Saboda lafiya ita ce arziki shi ya sa kamfanin ya bullo da sabon maganin mai suna Veggie Veggie, wanda yake maye gurbin kayan ’ya’yan ita ce da ganye a jikin dan Adam, musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa “Ba kowane jikin dan Adam ne ke iya tace abinci da kitse ba shi ya sa muka bullo da maganin Veggie-Veggie, wanda zai taimaka wa wajen tace abinci cikin sauki”.
Ya bukaci ’yan Najeriya su rika cin abinci mai inganci, wanda ya kunshi kayan gina jiki don samun koshin lafiya.
Mahalarta taron kaddamar da sabon maganin sun yaba wa kamfanin dangane da kokarin da yake yi na inganta lafiyar al’umma da bunkasar tattalin arziki ’yan Najeriya.