Wani kamfani zai samar da lantarki a Kano
Wani kamfani daga kasar Spain zai gina tasha®3r samar da wutar lantarki mai karfin Megawat 100 a Jihar Kano, domin inganta samar da wuta cikin sauki a jihar.Jakadan kasar, Mista Alfonso Sebestain ne ya sanar da haka, lokacin da ya kai ziyara ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a fadar gwamnati, inda ya bayyana cewa samun […]
Wani kamfani daga kasar Spain zai gina tasha®3r samar da wutar lantarki mai karfin Megawat 100 a Jihar Kano, domin inganta samar da wuta cikin sauki a jihar.
Jakadan kasar, Mista Alfonso Sebestain ne ya sanar da haka, lokacin da ya kai ziyara ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a fadar gwamnati, inda ya bayyana cewa samun wutar lantarki mai karfi za ta taimaka wajen farfado da masana’antu da kuma sauran sana’o’i da ke bukatar wutar lantarki a jihar.
Ya nuna cewa idan har Gwamnatin Kano ta samar da fili ga kamfanin, ko shakka babu za su gina wata katafariyar tasha, wadda za ta samar da wuta mai karfin Megawat 100 ba tare da gwamnati ta ba da komai ba, domin tallafa wa ci gaban rayuwar al’umma; musamman don bunkasa dogaro da kai.
Da yake mayar da jawabi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nuna godiyar al’ummar Jihar Kano dangane da yunkurin wannan kamfani wajen ganin jihar ta fita daga kangin rashin wadatar wutar lantarki.