Wani kamfanin Amurka ya zuba jarin Naira biliyan 200 don gina gidaje a Najeriya
Wani kamfani a Amurka mai suna Cantor Fitzgerald ya amince zai zuba jarin Naira biliyan 200 don samar da gidaje a Najeriya . Kamfanin na Amurka ya cimma yarjejeniyar zuba jarin ne da Kamfanin gina gidaje na Nigerian Mortgage Refinancing Company (NMRC) a ranar Talatar da ta gabata.bangarori biyun sun sanya hannu kan yarjejeniyar ne […]
Wani kamfani a Amurka mai suna Cantor Fitzgerald ya amince zai zuba jarin Naira biliyan 200 don samar da gidaje a Najeriya .
Kamfanin na Amurka ya cimma yarjejeniyar zuba jarin ne da Kamfanin gina gidaje na Nigerian Mortgage Refinancing Company (NMRC) a ranar Talatar da ta gabata.
bangarori biyun sun sanya hannu kan yarjejeniyar ne a hedikwatar Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da ke Abuja a kan idon Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iweala.
Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin NMRC, Farfesa Charles Inyangette ne ya sa hannu a madadin kamfanin NMRC, inda Manajin-Darakta Kamfanin Cantor Fitzgerald Mista Jack Heffernan ya sa hannu a madadin kamfaninsu.
Kamfanin ya amince zai gina gidaje dubu 10 a Kaduna da Legas da Enugu da kuma Abuja nan da badi.
Tuni kamfanin ya mallaki filayen da zai gina gidajen a jihohin da aka ambato a sama. Za a sayar da gidajen da kamfanin zai gina a kan farashin Naira miliyan 8 da Naira biliyan 15, inda wadanda za su mallaki gidajen za su iya biya a hankali tsawon shekara 20.
Za a fara aikin ginin gidajen a Legas a watan Afrilu mai zuwa.