Wani kasurgumin dan daba ya shiga hannun ’yan sanda

’Yan sanda a Jihar Kano sun tabbatar da kama wani da ake zargin kasurgumin dan daba ne mai suna Yunusa Ayuba da aka fi sani da kabusu wanda ya addabi mazauna yankin Sheka a kramar Hukumar Kumbotso da ke jihar.Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana wa manema labarai cewa […]

Wani kasurgumin dan daba ya shiga hannun ’yan sanda
Wani kasurgumin dan daba ya shiga hannun ’yan sanda

’Yan sanda a Jihar Kano sun tabbatar da kama wani da ake zargin kasurgumin dan daba ne mai suna Yunusa Ayuba da aka fi sani da kabusu wanda ya addabi mazauna yankin Sheka a kramar Hukumar Kumbotso da ke jihar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana wa manema labarai cewa ’yan sanda sun dade suna neman Yunusa tare da wadansu mutum biyu da suka hada da Anas Mai Dabba da Muhamamdu dan Zirge wadanda suka addabi jama’a da ayyukan ta’addanci.
A kwankin baya an zargin Yunusa kabusu da farke cikin wani abokin fadansa da almakashi lamarin da ya jawo ya rasuwarsa. Rahotanni sun ce bayan faruwar wancan kisa Yunsua kabusu ya gudu.
Majiya ya ce sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Rabi’u Yusuf ya fito da sabon shiri mai suna: “Duk dan da ya hana uwarsa barci, shi ma ba zai yi barci ba,” don yaki da harkar daba a jihar.
Majiya ya ce za su gurfanar da Yunusa kabusu a gaban shari’a don ya fuskanci hukunci kan zargin da ake yi masa. Ya ce wani daga cikin ’yan daban ya kai kansa ga ’yan sanda inda ya sallama makamansa tare da alkawarin daina harkar daba gaba daya.