…wani kuma ya yi wa mara lafiya fyade
Kotun Majistare Mai lamba 10 da ke Nomanslan ta bayar da umarnin tsare wani “likita” Ibrahim danjummai a gidan maza bisa zarginsa da yi wa wata marar lafiya mai suna Zulaiha Sagiru fyade a lokacin da ta je kemis dinsa domin neman magani. dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Shu’aibu Musa ya shaida wa […]

Kotun Majistare Mai lamba 10 da ke Nomanslan ta bayar da umarnin tsare wani “likita” Ibrahim danjummai a gidan maza bisa zarginsa da yi wa wata marar lafiya mai suna Zulaiha Sagiru fyade a lokacin da ta je kemis dinsa domin neman magani.
dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Shu’aibu Musa ya shaida wa kotu cewa tun da farko, mijin matar, Sagiru Buhari na garin Kafin Agur ya kai kara ofishin ’yan sanda na Madobi, cewa wani “likita” da ke da shagon sayar da magunguna ya yi wa matarsa fyade a lokacin da ta je kemis. “A wannan lokaci ne kai Ibrahim danjummai ka yaudare ta ta hanyar shasshafa mata jiki, har a karshe ka yi mata fyade.”
Takardar karar ta ci gaba da cewa: “Bayan faruwar lamarin ne marar lafiyar ta dawo hayyacinta, inda ta shiga dimuwa da damuwa har ta je ta sanar da mijinta.”
Sai dai wanda ake zargin, wanda kuma bincike ya gano cewa ba likitan gaskiya ba ne yana yin sojan gona ne kawai a yankin nasu, inda yake nuna kansa a matsayin kwararren likita, ya musanta laifukan da ake zarginsa da shi na fyade da sojan gona; laifukan da suka saba wa sashe na 187 da 235 na Kundin Shari’a na Finalkod.
Mai shari’a Maryam Ahmad Sabo ta bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a kurkuku har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba, inda za a ci gaba da sauraren shari’ar.