Wani likita ya kamu da cutar Ebola a Sierra Leone
Fadar shugaban kasar Sierra Leone ta bayyana cewa likitan da ke jagorantar yaki da annobar Ebola a kasar ya harbu da kwayar cutar kuma yana karbar kulawa a wani asibiti.An fahimci cewa likitan mai suna Sheikh Umar Khan ya kamu da cutar ne bayan da akai masa kwajin da ya tabbatar da ita a jikinsa […]
Fadar shugaban kasar Sierra Leone ta bayyana cewa likitan da ke jagorantar yaki da annobar Ebola a kasar ya harbu da kwayar cutar kuma yana karbar kulawa a wani asibiti.
An fahimci cewa likitan mai suna Sheikh Umar Khan ya kamu da cutar ne bayan da akai masa kwajin da ya tabbatar da ita a jikinsa amma yanzu yana kwance a asibitin garin Kailahun, inda cutar ta fara barkewa a kasar. Sanarwar ta bayyana likitan da wani gwarzo wanda ya sadaukar da kansa wajen yaki da annobar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa Ministar Kiwon Lafiyar kasar Miatta Kargbo tana hawaye a lokacin da ta samu labarin. Ta ce za ta yi dukkannin abun da ya dace don tabbatar da cewa cutar ba ta yi ajalinsa ba.
Wakilin BBC Umaru Fofana da ke babban birnin kasar, Freetown ya ce dimbin ma’aikatan lafiyan asibitin garin Kenema ne suka shiga yajin aiki a ranar Litinin, saboda mutuwar wasu abokan aikinsu uku da suke zargin sun mutu ne daga cutar.
Mutum dai fiye da 630 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar a kasashen Afirka uku tun lokacin da annobar ta fara a kasar Guinea a watan Janairun da ya wuce. Kuma 206 daga cikinsu daga kasar Sierra Leone ne.