Wani lokaci ’yan dambe sukan kai mana naushi – Mawakin Dambe

Fitaccen makadin dambe wanda ake kira Halilu Wazirin Ibrahim Karakai ya ce duk da sabon da suka yi wa ’yan dambe, wani lokaci sukan kai musu bugu idan rana ta baci.Halilu wanda ya shafe shekaru fiye da 30 yana wakar dambe ya shaida wa Aminiya a Legas cewa ba kowane lokaci ’yan damben ke kai […]

Wani lokaci ’yan dambe sukan kai mana naushi – Mawakin Dambe

Halilu Wazirin Ibrahim Karakai a lokacin da yake yin waka tare da yaransa. Fitaccen makadin dambe wanda ake kira Halilu Wazirin Ibrahim Karakai ya ce duk da sabon da suka yi wa ’yan dambe, wani lokaci sukan kai musu bugu idan rana ta baci.
Halilu wanda ya shafe shekaru fiye da 30 yana wakar dambe ya shaida wa Aminiya a Legas cewa ba kowane lokaci ’yan damben ke kai musu duka ba sai rana ta baci.
 Ya ce: “Gaskiya idan aka yi rashin sa’a wani dan damben yakan kai duka amma idan mawaki a shirye yake ba zai iya samunsa ba idan kuwa mawaki ba shi da shiri, ai ka ga dole a same shi. Amma mu da yardar Allah babu yadda za a yi su same mu. Ka san shi wasa irin na dambe ba a yin sa sai da shiri. Hakazalika kai ma mai kida da waka dole sai ka shirya. Amma duk da haka ba kowane lokaci hakan take faruwa ba kuma ba duk dan dambe ne yake kai duka ba.”
Halilu wanda ya ce ya gaji kidan ne daga wurin mahaifinsa ya dage a kan cewa ya sami nasarori da yawa a harkar kida da wakar dambe.
Makadin na dambe, shi dan asalin kauyen Karakai ne a karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara. Ya ce tun yana karami ya koyi kida da wakar dambe. Ya kara da cewa: “Babu salon kida da wakar damben da ban iya ba. Da na kalli dan dambe sai kawai salon wakar da nake so na yi masa ta zo mini a raina ba tare da wata wahala ba. Saboda haka da na fara waka su kuma makidana sai su fara kida. Idan kuma sun kasa, ni sai na karba na gwada musu yadda za su yi.”
Ya bayyana cewa yana kida ga ’yan damben Kudu da Guramada da kuma Jamus.
Ya kara da cewa ya sami nasarori da yawa wadanda suka hada da mallakar mashin biyu a garin Abuja da gida a Jihar Katsina.
“Sai dai mu yi wa Allah godiya, domin a shekara 36 da na yi ina kida da wakar dambe, na sami nasarori da dama da ba za su kirgu ba. Muna samun na abinci da sutura har ma mu yi kyauta ga ’yan uwa da abokan arziki.”
Ya bayyana cewa burinsa ya zama ya yi fice a harkar kida da wakar dambe a Najeriya gaba daya.