Wani magidanci ya kashe saurayin matarsa a Adamawa

Magidancin ya shaida wa kotu cewa ya sha gargadin mamacin cewa ya daina bin matarsa, amma ya ki ji

Wani magidanci ya kashe saurayin matarsa a Adamawa

An gurfanar wani magidanci a kotu bisa zargin ya kashe wani matashi da yake zargi yana neman matarsa a Jihar Adamawa.

Ana zargin magidancin da hada kai da kaninsa wajen lakada wa mamacin duka har lahira ne bayan da ya kama su tare da amaryar tasa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Zakka Musa ya shaida wa kotu cewa magidancin da dan uwan nasa sun far wa mamacin ne da adduna da sanduna, suka yi ajalinsa; an kai shi asibitin da ke garin Fufore, amma likitoci suka ce ya riga ya rasu.

Amma da yake ba da bahasi, magidancin mai shekaru 20 ya shaida wa kotu cewa ya sha jan kunnen mamacin cewa ya daina neman matarsa, amma ya ki ji.

Ya ce fada ne ya kare a tsakaninsu, bayan sun bi sawun mamacin suka kama shi tare da amaryar tasa da aka daura musu aure bara.

A cewarsa, mamacin ne ya fara bugun sa da sanda, shi ne kaninsa ya kawo masa dauki, suka ga bayansa, amma ya musanta cewa sun yi amfani da adda a lokacin fadan.

Bayan sun amsa zargin ne Babbar Kotun Majistare da ke Yola ta sa a tsare su zuwa ranar 27 ga watan nan na Yuli.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja