Wani magidanci ya yi wa ’yar wansa ciki
Ana zargin wani magidanci mai suna Haruna Adamu da ke zaune a Suleja ta Jihar Neja da yi wa ’yar wansa marainiya ciki.Mahaifiyar yarinyar Jummai Muhammadu Sani ce ta kai karar kanen tsohon mijinta da suke uwa daya uba daya ga ’yan bangar masarautar Suleja, inda ta ce, mutuwa ce ta raba ta da wan […]
Ana zargin wani magidanci mai suna Haruna Adamu da ke zaune a Suleja ta Jihar Neja da yi wa ’yar wansa marainiya ciki.
Mahaifiyar yarinyar Jummai Muhammadu Sani ce ta kai karar kanen tsohon mijinta da suke uwa daya uba daya ga ’yan bangar masarautar Suleja, inda ta ce, mutuwa ce ta raba ta da wan wanda take kara. Kuma bayan rasuwar mijinta ne, ta yi aure a Katsina inda ta tafi ’ya’yansu uku, amma wanda take kara da wasu daga cikin ’yan uwansa da suka hana ta gadon ’ya’yanta ya rika yi mata barazanar karbar ’ya’yan bayan ya zarge ta da kashe daya daga cikinsu.
Jummai ta ce ta kai shi kotu amma kafin nan ta turo yarinyar Suleja don ta yi huta ta ga dangin mahaifinta inda wanda ake zargin ya yaudari yarinyar ya yi mata fyade.
Da Aminiya ta tuttubi yarinyar (an sakaya sunanta) mai shekara 15 da ke dauke da cikin wata hudu, ta ce kanen mahaifin nata yakan tursasa ta, ya kwanta da ita tare da yi mata gargadin kada ta fada wa kowa. “Ya ce in na fada kunya tawa ce shi ko kadan ba zai ji kunya ba kuma har sau uku ya kwanta da ni,” inji ta
Wanda ake zargin, Haruna Adamu ya amince a gaban ’yan banga cewa cikin nasa ne sai dai ya ce laifin yarinyar ce da Shaidan. Ya zargi yarinyar da cewa ita ce ke zuwa dakinsa ba tare da sutura a jikinta ba inda ya ce ya gargade ta amma ta ki sai Shaidan ya zuga shi. “Kuma sau daya kadai na kwanta da ita,” inji Haruna.
Jami’in gudanarwa na ’yan bangar Malam Aminu Ibrahim Baba ya ce daga bayanin mahaifiyar yarinyar ya nuna cewa Haruna da ’yan uwansa sun so a zubar da cikin amma sun bar wa mahaifiyar yarinyar nauyin sannan shi Haruna ya biyo ta har gida yana ci mata mutunci wanda ya sa ta kawo kara. Ya ce za su tura maganar zuwa kotun shari’ar Musulunci.