Wani mahaifi ya karbi Naira 40 a matsayin sadakin ’yarsa

Wani uba a kasar Saudiyya ya karbi Riyal daya, wanda ya yi daidai da Naira 40 a matsayin sadakin auren ‘’yarsa. Mahaifin amaryar ya yanke wannan hukuncin ne, lokacin da ya samu labarin angon ya yi hadarin mota kuma an sace masa kudin da ya fitar daga banki don ya biya sadakin aurensa.Da ango ya […]

Wani mahaifi ya karbi Naira 40 a matsayin sadakin ’yarsa

Wani uba a kasar Saudiyya ya karbi Riyal daya, wanda ya yi daidai da Naira 40 a matsayin sadakin auren ‘’yarsa. Mahaifin amaryar ya yanke wannan hukuncin ne, lokacin da ya samu labarin angon ya yi hadarin mota kuma an sace masa kudin da ya fitar daga banki don ya biya sadakin aurensa.
Da ango ya fahimci ya yi asarar kudinsa, sai ya roki matar da zai aura kan lallai ta roki iyayenta a daga ranar aurensu, zuwa nan da shekara daya. Jin halin da ake ciki, sai mahaifin amaryar ya dage kan cewa ba za a daga auren ba. Don haka sai ya bukaci surukinsa ya biya sadakin Riyal daya kawai, a matsayin sadakin aurensa.
Masu mu’amala da kafofin shafukan sadarwar intanet, sun yi ta sanya wa uban amarya albarka. Jaridar Gulfnews ta ruwaito labarin, amma ba ta ambaci sunayen mahaifin amarya da ango da amaryarsa ba.
A kasashen, musamman wadanda suke yankin tekun Fasha, ana fama da matsalar tsadar aure. Don haka malamai suka yi ta kokarin ganin sun rage sadaki, amma al’amarin ya ci tura.