Wani makaho ya sha alwashin zama dan jarida

Ganin cewa aikin jarida aiki ne mai matukar hadari da kuma kalubale wanda masu ido ma suna fuskantar matsaloli balle marasa ido, amma sai ga wani makaho mai suna Aliyu Muhammad Mustapha, dan asalin Jihar Kaduna wanda yake da zama a garin Kano ya kuduri aniyar zama dan jarida mai karanta labarai a gidan rediyo. […]

Wani makaho ya sha alwashin zama dan jarida
Wani makaho ya sha alwashin zama dan jarida

Ganin cewa aikin jarida aiki ne mai matukar hadari da kuma kalubale wanda masu ido ma suna fuskantar matsaloli balle marasa ido, amma sai ga wani makaho mai suna Aliyu Muhammad Mustapha, dan asalin Jihar Kaduna wanda yake da zama a garin Kano ya kuduri aniyar zama dan jarida mai karanta labarai a gidan rediyo.

A lokacin da yake zantawa da Aminiya, ya bayyana dalilansa na yunkurin zama dan jarida. Ya ce ya jima yana son ya zama dan jarida saboda ya dinga karanta labarai a gidan rediyo amma bai samu dama ya yi karatu ba sai yanzu da ya shiga Kwalejin Koyon Aikin Shari’ar Musulunci ta Malam Aminu Kano, bangaren koyar da aikin jarida, don ya samu ilimin aikin.
Ya ce shi bai fuskantar kowace irin matsala, kasancewarsa makaho wanda yake karatu a tsakanin masu ido. Ya ce shi ba rubutu yake yi ba, yana daukar karatun ne a rikoda, idan ya koma gida ya rubuta da keken rubutu irin nasu na makafi, sannan ya karanta ya rike a kwakwalwarsa.
dalibin ya kara da cewa babban burinsa shi ne ya zama dan jarida mai karanta labarai yana wayar da kan al’umma ta hanyar labarai sannan kuma ya je ya dauko labaran da kansa ya rubuta ya kuma karanta. “Abin da ya sa nake son ya zama mai labarai a gidan rediyo ba a jarida ba shi ne, domin rediyo ya fi saurin fadakar da jama’a a kan jarida, wanda mutum ko a kauye yake zai iya jin labarai da ’yar karamar rediyonsa, sabanin jarida da kafin mutum ya san abin da ke faruwa sai an kwana kuma ba kowa ke iya sayen ta ba.”
Ya ce duk da ba shi da ido kamar sauran mutane amma ba ya jin cewa zai samu matsala a wannan aikin, domin ya jima yana sha’awar son zama dan jarida; tun da yana da sha’awar hakan, ya san ba zai fuskaci kalubalen da ake magana a kai ba. Sannan sai ya bai wa sauran masu nakasa irinsa shawarar cewa kar su kashe zuciyarsu wajen yin bara, su tashi su nemi ilimin zamani, wanda zai ba su dama su dogara da kansu.