Wani malami ya fara gina babbar makarantar Islamiyya a Ibadan

Shugaban Makarantar Ummulkitab Islamic School da ke unguwar Sabo cikin birnin Ibadan, Ustaz Hafiz Shehu Usman, ya fara aikin gina sabuwar makaranta mai suna Hafiziyyah Islamic Foundation da za a kashe kudi fiye da Naira miliyan 50 wajen ginawa da samar da kayan aikin koyarwa na zamani. Makarantar za ta kunshi azuzuwan koyarwa na sashen […]

Wani malami ya fara gina babbar makarantar Islamiyya a Ibadan
Wani malami ya fara gina babbar makarantar Islamiyya a Ibadan

Shugaban Makarantar Ummulkitab Islamic School da ke unguwar Sabo cikin birnin Ibadan, Ustaz Hafiz Shehu Usman, ya fara aikin gina sabuwar makaranta mai suna Hafiziyyah Islamic Foundation da za a kashe kudi fiye da Naira miliyan 50 wajen ginawa da samar da kayan aikin koyarwa na zamani.

Makarantar za ta kunshi azuzuwan koyarwa na sashen renon kananan yara da firamare da sakandare da za a samar da manhajar karatun harshen Larabci da ilmin addinin Islama tare da ilmin boko.
Wakilinmu da ya ziyarci aikin ginin sabuwar makarantar ya gano cewa an dakatar da aiki na tsawon lokacin watan azumin Ramadan da za a ci gaba da aikin, bayan Sallah. Amma zuwa yanzu an kammala kashi 40 daga cikin 100 na ayyukan gini baki daya.
Da yake nuna wa wakilinmu irin nasarorin da aka samu a kan wannan muhimmin aiki, Ustaz Hafiz Shehu Usman ya ce, ya fara sha’awar yin wannan aiki daga aljihunsa ne a dalilin rashin dakin karatu (laburare) a cikin makarantar Ummulkitab Islamic School kuma babu dakin koyarwa da na’urorin kwamfuta ta hanyar zamani. “Wanda Allah Ya taimaka muka sayi wannan babban gida, muka rushe domin gina sabuwar makaranta da za a samar da wadannan muhimman abubuwan koyarwa domin amfanin al’ummar Musulmi da ke zaune a ciki da wajen wannan unguwa ta Sabo.” Inji shi.
Muhimman abubuwan da za a tanada a cikin makarantar mai bene hawa daya, sun hada da masallaci da babban zauren taro da azuzuwan kananan yara da azuzuwan manyan mutane da kuma ofishin makaranta da babban dakin karatu (laburare). “Ba mu taba samun laburare a cikin wannan unguwa ba duk kuwa da girma da yawan jama’arta. Wannan ya karfafa min gwiwa wajen sayan wannan wuri domin gina sabuwar makarantar da za a tanadar mata irin wadannan muhimman abubuwan koyarwa. Ina matukar farin ciki da samun wannan damar cin ma burin gina dakin karatu a cikin unguwar Sabo. Haka kuma, mun kebe dakunan koyarwa da na’urorin kwamfuta domin yin bincike a kan abubuwa da suka shafi addinin Musulinci da sauran fasahar zamani. Akwai wasu muhimman tsare-tsare da muka yi a kan koyarwa ta hanyar amfani da kwamfuta wanda ba zan yi dogon bayani a kai ba sai mu roki Allah Ya nuna mana lokacin da za mu bude wannan makaranta domin cin ma buri.”
Da yake amsa wata tambaya, Ustaz Hafiz Shehu Usman ya ce, yau shekaru 20 da wucewa ke nan da Allah Ya dawo da zamansa a cikin unguwar Sabo Ibadan daga mahaifarsa da ke garin Jos. Ya ce tun daga wancan lokaci yake gudanar da aikin koyar da Alkur’ani ga almajiransa. “Ina son ka gane cewa, al’ummar da ke zaune a wannan unguwa ta Sabo, su ne suke bi na bashi, wannan ne dalilin da ya sa nake so in biya su da koyarwar ilmin addinin Islam da na zamani ba tare da sun biya ko kwabo a matsayin kudin makaranta a cikin sabuwar makarantar da muke ginawa ba. Duka wadannan tsare-tsare, na shirya su ne ta hannun sakataren makaranta, Alhaji Bala Hashimu wanda nake jinjina masa a kan sadaukar da kansa wajen ganin mun tafi tare domin tsira tare da cin ma buri.” Inji malamin.