Wani matashi a kasar Sin ya jefa kansa gidan damisa
Wani matashi da ke zaman kashe wando a kasar Sin ya yi yunkurin mika kansa ga damisa ta cinye shi, inda aka ceto shi da kyar. Jaridar Chengdu Business Daily, ta ruwaito cewa amtashin dan shekara 27 ya hau kan wata doguwar bishiya inda ya fada cikin gidan damisa, a gidan namun daji da ke […]
Wani matashi da ke zaman kashe wando a kasar Sin ya yi yunkurin mika kansa ga damisa ta cinye shi, inda aka ceto shi da kyar. Jaridar Chengdu Business Daily, ta ruwaito cewa amtashin dan shekara 27 ya hau kan wata doguwar bishiya inda ya fada cikin gidan damisa, a gidan namun daji da ke Chengdu da ke garimn Sichuan, a Kudu maso Kudancin kasar Sin.
Masu kallon namun daji sun cika da mamaki ganin yadda matashi Yang, wanda bas hi da aikin yi, ya jefa kansa cikin dakin damisa, ind aya shafe mintuna 20, yana ta kokarin jawo hankalin damisar kan cewa lallai ta zo ta cinye shi.
“Na roki damisoshi su cinye ni, su ci nama na, kuma ba na shirin fada don kare kaina,” a cewar Yang kamar yadda bayyana wa jaridar.
Duk da cewa damisa ta kama shi, ta ja shi ta baya, sai kuma ta ki cin namansa. Nan da nan ma’aikatan gidan namun dajin suka lallabi damisar, ta ba su dama suka ceto Yang, wanda ya yi fama da raunuka 16,” kamar yadda rahoto ya nuna.