Wani matashi da ya kashe matar da ya gada ya yi yunkurin halaka kansa
Wani mtashi mai shekara 37 wanda ake zargi da kashe matarsa da ya gada daga marigayi yayansa, ya yi yunkurin halaka kansa, bayan da jami’an tsaro sun kama shi bayan da ya aikata wannabn ta’asa. Matashin mai suna Shaibu Buba ana zargin ya halaka matar da ya gada daga dan uwansa ta mummunar hanyar azabtarwa. […]

Wani mtashi mai shekara 37 wanda ake zargi da kashe matarsa da ya gada daga marigayi yayansa, ya yi yunkurin halaka kansa, bayan da jami’an tsaro sun kama shi bayan da ya aikata wannabn ta’asa.
Matashin mai suna Shaibu Buba ana zargin ya halaka matar da ya gada daga dan uwansa ta mummunar hanyar azabtarwa.
Buba ya yi ta dukan matar mai suna Satina buba, mai shekara 45 har ta mutu, inda ya sassareta da adda tana barci. Satina dai tna da ’ya’ya hudu da ta haifa wa marigayi mijintta danladi, wanda ya mutu a bara (shekarar 2016).
Bisa al’adar akl’ummarsu, Shaibu ya gaji Satina bayan ya cika sharuddan al’adar aure cikin watan Fabrairun bana, sannan ya tare da ita a Kuruduma II, wani yanki na rukunin gidajen Asokoro da ke babban birnin tarayya Abuja.
Daga bisani ya samu labarin tana mu’amala da wnai mutum. Maimakon ya yi bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin, sai ji aka yi ya yanke hukuncin halakata, kamar yadda Kwamishinan ’yan sanda Mohammed Sadik Bello ya bayyana wa manema labarai, inda a cewarsa, ‘ya sassara matar ranar wata 16 ga Nuwambar bana da adda ya ji mata mummunan rauni wajen karfe hudu da rabi na dare.
A sashen binciken miyagun laifuka na ofishin (CID) ’yan sanda da ke Abuja, Shaibu, wanda asalinsa dan karamar Hukumar Shonmou ne da ke Jihar Gombe ya ce: “Na kashe matata da na gada daga marigayi dan uwana, danladi Buba, wanda ya mutu a bara. Marigayiya matata ta Haifa wa danladi ’ya’ya hudu. Cikin watan Fabrairun bana na gajeta bisa amincewa iyalanmu.
“Na halakata ne ta hanyar dukanta da sanda lokacin da take barci. Na samu labari daga mutane cewa matata tana mu’amala da wani mutumin..”
Da ya fahimci mummunan aikin da ya aikata, sai ya shiga daklin girki, inda ya yi yunkuri halaka kansa. Ya bulbula kanazir a jimkinsa, sannan ya kunna wa klansa wuta, daga bisani aka yi saurin kai shi wajen ’yan sandan Asokoro, ya kuma mika kansa da kansa.
’Yan sanda sun bi Kadin lamarin zuwa gidansa, inda suka yi kokarin ceto matarsa, har suka kaita asibitin Asokoro, inda daga bisani ta mutu.
Bayan mutuwar matar ne, aka tsare Shaibu a ofishin ’yan sanda na Asokoro. “Na yi nadamar mummunan aikin shaidan da na aikata.,” inji Shaibu.
Daga bisani ‘’yan uwan Satina sun gabatar wa ’yan sanda kwararan hujjoji, inda suka bukaci a ba su gawar ’yarsu don su yi mata jana’iza.Mahaifin Satina, ya ce: “’yar mu na da ’ya’ya hudu daga marigayin mijinta. Bayan mutuwarsa, sai ta amince dan uwansa kanensa ya gajeta kamar yadda ka’idar al’adarmu ta shimfida. Shaibu ya je Gombe a janairun 2017 don gudanar da al’adun sake auren ’yata a Fabrairun bara.
Bello ya tabbar da cewa iyayen mamaciyar sun bukaci ’yan sanda su ba su gawar bayan sun kamala binciken laifin kisan gillar.