Wani matashi ya farke cikinsa saboda ya kamu da cutar kanjamau

A ranar Alhamis din makon jiya ne mutanen garin Samaru da ke karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna suka shiga jimami a lokacin da suka samu labarin wani matashi ya farke cikinsa da wuka ya mutu saboda ya kamu da cutar kanjamau.Wakilinmu wanda ya ziyarci gidan su marigayin mai suna Oluwa Sogo Ayeni mai […]

Wani matashi ya farke cikinsa saboda ya kamu da cutar kanjamau

Mohammed D. Abubakar Sufeto Janar na ‘Yan sandan NajeriyaA ranar Alhamis din makon jiya ne mutanen garin Samaru da ke karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna suka shiga jimami a lokacin da suka samu labarin wani matashi ya farke cikinsa da wuka ya mutu saboda ya kamu da cutar kanjamau.
Wakilinmu wanda ya ziyarci gidan su marigayin mai suna Oluwa Sogo Ayeni mai shekara 32 da ke Layin Na’ibi a Samaru, ya tarar da jama’a da dama cikin juyayi, inda wandanda suka ga lamarin suka shaida masa cewa an samu gawar Olowa Sogo ne a rigingine, cikinsa a farke da wuka rike a hannu dammarsa.
Shaidu sun ce marigayi Oluwa ya fara yanka wuyarsa ne, kafin ya dawo cikinsa ya farde, har kayan cikinsa ya fito waje.
’Yar uwar marigayin mai suna Misis Jimoh da suke uwa daya uba daya, ta shaida wa wakilinmu cewa marigayi Oluwa yana aikin gadi ne a Jihar Katsina kuma ya dawo gida ne kamar wata daya da ya wuce saboda rashin lafiya.
Ta ce ya je Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika domin a gano abin da ke damunsa, inda a karshe aka gane cewa yana dauke da cutar kanjamau na, sai aka rubuta masa magunguna domin ya je ya saya.
Malama Jimoh ta ce bayan marigayi Oluwa ya dawo da takardar maganin, “Ni da sauran ’yan uwana muka hada masa Naira dubu biyar domin ya je ya sayi maganin, saboda ya ce ciwon yana damunsa. “To bayan mun hada masa kudin a ranar Laraba sai kawai muka wayigari ranar Alhamis ya kashe kansa,” inji ta.
Da wakilinmu ya tambaye ta ko mutane sun fara nuna masa kyama ne? Sai Malama Jimoh ta ce ba wanda ya nuna masa kyama, domin ba kowa ya san yana da wannan ciwo ba. Ta kuma musanta jita-jitar da mutane ke yadawa cewa wai kafin dan uwanta ya kashe kansa sai da ya tattara kayansa duk ya kone. “Wannan ba gaskiya ba ne, domin kuwa duk kayansa na nan, ni na tattara su da hannuna har da katinsa na karbar kudi a banki da duk takardunsa a bayan rasuwarsa, in akwai kayan da ya kona to irin wadanda ba ya so ne, kuma bai nuna mana alamun cewa ze kashe kansa ba, na yi bayani a baya cewa mun tara masa kudi domin ya sayi magani, wanda ka yi wa haka ai ba za ka sa ran zai yi abin da ya yi ba,” inji ta.
A lokacin da wakilinmu ya yi kokarin ganawa da iyayen marigayi Oluwa, sai aka ce an ba su maganin barci domin tunda lamarin ya faru ba su samu yin barci ba saboda firgici.
A lokacin da Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rudunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Aminu Lawal sai waya ta tsinke, sai dai wani dan sanda da bai so a ambaci sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin.