Wani matashi ya yanke harshen baffansa

A ranar Litinin din da ta gabata ne jama’ar garin Dausayi a karanmar Hukumar Gezawa, Jihar Kano suka tashi da alhinin yanke wa wani dattijo harshe da wani dan dan uwansa ya yi. Lamarin ya faru ne a lokacin da dattijon mai suna Malam Shu’aibu Dausayi mai kimanin shekara 75 yake kwance a gado a […]

Wani matashi ya yanke harshen baffansa
Wani matashi ya yanke harshen baffansa

A ranar Litinin din da ta gabata ne jama’ar garin Dausayi a karanmar Hukumar Gezawa, Jihar Kano suka tashi da alhinin yanke wa wani dattijo harshe da wani dan dan uwansa ya yi.

Lamarin ya faru ne a lokacin da dattijon mai suna Malam Shu’aibu Dausayi mai kimanin shekara 75 yake kwance a gado a dakinsa inda wani matashi mai suna Jamilu Inusa wanda dan kanen Malam Shu’aibu ne ya shiga dakin ya danne shi ya sa wuka ya yanke harshensa ya tafi da shi.
Malama Fatima Shu’aibu uwargidan Malam Shu’aibu ta ce “Muna zaune a tsakar gida Jamilu ya shigo gidan, to kasancewarsa da ne a gidan ba mu yi zaton wani abin assha zai aikata ba, sai ya shiga dakin Malam ya tarar da shi kwance a gado. Ya shake shi ya bude masa baki ya sa wuka ya yanke masa harshe. Mu dai ihunsa muka ji, ga shi a lokacin ba kowa a gidan sai mu mata kawai,” inji ta.
Yanzu haka dattijon na kwance a Asibitin Malam Aminu Kano, kuma wani likitan asibitin Dokta Kelibin ya ce da daga yanke harshen an sanya a cikin kankara, da za a iya mayar masa da ita.
An ce an binne harshen a can garinsu inda daruruwan jama’a suka halarta tare da yin Allah wadai da ta’addancin da matashin ya yi ga baffansa.
A yayin da wasu ke zargin tsafi matashin zai yi da harshen, wata majiya a Dausayi ta ce akwai jikakkar rikicin gidan gado a tsakanin matashin da baffansa. Sai dai matar dattijon ta ce, “Batun rigimar gadon gida bai taso ba, domin mahaifin matashin ma ba ya da gado a gidan. Malam ne ya ji tausayinsa ya taimaka masa da dan fili a gidan, amma sai ga shi ya yi masa sakayya ta wannan hanya.”
Kakakin’Yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da kame Jamilu inda ya ce, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya bayar da umarnin a tsare shi a sashin binciken manyan laifuffuka don ci gaba da bincike kan lamarin.