Wani matashi yana daukar kansa hoto sau 200 a rana

Wani matashi mai suna Junaid Ahmed yana daukar kansa a hoto (selfie) har sau 200 a kowace rana, inda yake sanyawa a kafofin sadarwa na zamani. Junaid Ahmed yana da mabiya dubu 50, a shafin sada zumunta na Instagram kuma ya ce yana jin dadin daukar hoton kansa sosai kamar yadda kafar labarai ta BBC […]

Wani matashi yana daukar kansa hoto sau 200 a rana

Wani matashi mai suna Junaid Ahmed yana daukar kansa a hoto (selfie) har sau 200 a kowace rana, inda yake sanyawa a kafofin sadarwa na zamani.

Junaid Ahmed yana da mabiya dubu 50, a shafin sada zumunta na Instagram kuma ya ce yana jin dadin daukar hoton kansa sosai kamar yadda kafar labarai ta BBC ta ruwaito.

Junaid Ahmed matashi ne mai kimain shekara 22 a duniya, kuma ya yi fice matuka a kafofin sadarwar saboda yawan mabiyansa. Yana mayar da hankali wajen zabar lokacin da zai sanya hoto a kafofin sada zumunta saboda ya samu mutane da yawa su yaba hoton, kuma idan mutane kasa da 600 suka yaba hoton, yana cirewa saboda rashin yawansu.

Junaid Ahmed ya ce: “Idan na saka hoto, to a minti biyu na farko ina samun kamar mutum 100 da za su yaba kuma abin yana faranta mini rai sosai.” 

Wani binciken da aka yi a baya-bayan nan a Jami’ar Nottingham Trent ya nuna cewa masu daukar hotunan kansu suna fama da wani ciwo ne mai alaka da tabin hankali da ake kira Selfitis. Shi wannan ciwo na selfitis yana sanya mutum ya zama mai yawan sha’awar daukar kansa hoto duk da cewa ba a dade da gano ciwon ba.

Junaida ya ce yawan son daukar hoton kansa da yake yi yana jawo masa rashin jituwa a tsakaninsa da masu kaunarsa. Ya ce a yanzu irin maganganun kushe da ake yi kan hotunansa ba sa damunsa kamar da -amma ya fallasa cewa an yi masa tiyatar kwaskwarima a fuska saboda matsin lambar da yake fuskanta daga kafofin sada zumunta.

Ya ce an mayar masa da hakoransa farare an gyara masa haba da kumatu da muka-muki da lebba da kasan ido da kai da sanya masa gashin ido da kuma rage masa kiba.

Junaid wanda dan birnin Essed ne na kasar Ingila ya ce ya fahimci yadda mutum zai iya haduwa da adawa a kafofin sada zumunta, amma bai damu ba sosai.

Kuma ya ce abubuwan da muke gani a kafofin sada zumunta ba gaskiya ba ne.

“Kafofin sada zumunta suna da dadin amfani, amma kada ku bari su shafi rayuwarku ta wajen son zama abin da kuka ga wadansu sun zama.”

 

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu