Wani ministan Jonathan ya saci kusan Naira tirilyan daya da rabi – Oshiomhole

Manyan jami’an kasar Amurka sun shaida wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon jiya cewa wani minista a gwamnatin Goodluck Jonanathan shi kadai ya saci Dala biliyan shida (kimanin Naira tiriliyan daya da biliyan 380). Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, wanda ke cikin wadanda suka yi wa Shugaba Buhari rakiya zuwa Amurka ne ya bayyana […]

Wani ministan Jonathan ya saci kusan Naira tirilyan daya da rabi – Oshiomhole
Wani ministan Jonathan ya saci kusan Naira tirilyan daya da rabi – Oshiomhole

Manyan jami’an kasar Amurka sun shaida wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon jiya cewa wani minista a gwamnatin Goodluck Jonanathan shi kadai ya saci Dala biliyan shida (kimanin Naira tiriliyan daya da biliyan 380).

Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, wanda ke cikin wadanda suka yi wa Shugaba Buhari rakiya zuwa Amurka ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai na fadar Shugaban kasa, sai dai bai bayyana sunan ministan ba.
Oshiomhole yana mayar da martani ne kan sukar da jam’iyyar adawa ta PDP ke yi kan ziyarar Shugaba Buhari na wuni hudu a kasar Amurka.
Ya ce, “…Akwai bukatar a tausaya musu (PDP). Muna da Shugaban kasa da yake magana da karfin gwiwa; ba Shugaban kasar da zai rika surkulle bai da tabbacin a kan me yake magana ba. Shi (Buhari) mutum ne da zai gaya wa Majalisar Dattawan Amurka cewa “Najeriya ana tafiyar da ita ne a kan doka.’ Ba za mu yi wani abu da ya saba wa al’adu da dabi’un mutanenmu ba. Mun rabu da Shugaban kasar da bai san karfin ikonsa ba, zuwa ga Shugaban kasar da ya fahimci shi shugaban wata kasa ce a a Afirka. To me kuke sa rai PDP ta ce? Na sha fadi duk ranar da kuka ga ’yan fashi suna yin tafi, to ku sani abubuwa suna tafiya ba daidai ba. Lokacin da kuka gan su (PDP) suna firgita, ku sani hukumomin tsaro suna bakin kokarinsu. PDP ta kashe kasar nan.”
Ya kara da cewa: “Ina nufin daga bakunan jami’an Amurka; manyan jami’an harkokin kasar, sun ce wani minista a karkashin PDP ya karkatar da abin da ya kai Dala biliyan shida, kuma sun ce ko a matsayi irin na Washington wannan abin girgiza ne.”