Wani mutum ya guji dansa ya samu mukami a Ekiti
Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya bai wa wani mutum da ya guji dansa aiki a matsayin Jakadan Yaki da Annobar Coronavirus na jihar Ekiti. Mutumin mai suna Mista Adeoye ya guji dan nasa ne, inda ya hana shi shiga gidan sa, ya ce jami’an Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) a […]
Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya bai wa wani mutum da ya guji dansa aiki a matsayin Jakadan Yaki da Annobar Coronavirus na jihar Ekiti.
Mutumin mai suna Mista Adeoye ya guji dan nasa ne, inda ya hana shi shiga gidan sa, ya ce jami’an Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) a jihar Ekiti su rike yaron su killace shi.
A fafen bidiyon da wani jami’in hukumar ta NCDC a jihar Ekiti ya dauka ya sanya a kafar sada zumunta an ga mahaifin yaron yana bayanin cewa a lokacin da dan nasa zai tafi jihar Legas, ya hana shi zuwa saboda gudun kar ya dauko annobar.
Yace yaron yaki jin maganarsa ya tafi abinsa, ” lokacin da ya kirani ya ce min yi taso daga Legas zai dawo gida, motar da ya shigo ta sauke shi a Abeokuta, sai na fada masa ya koma inda ya fito domin ba zan karbe shi ba, amma duk da haka yaki ji” inji shi.
Ya kara da cewa ” da naga haka sai na baiwa jami’an Hukumar NCDC lambobin wayar salularsa biyu na shaida masu halin da ake ciki inda na nemi su tsare shi idan ya shigo Ekiti suyi masa gwajin coronavirus” inji shi.
A faifen bidiyon an jigo jami’in na NCDC yana fadawa mahaifin yaro cewa mun yiwa danka gwaji lafiyar sa kalau dan haka ka tafi da shi gida, yayin da uban ya tubure yace afafau dan nasa ba zai bar dan ya shiga gidan saba.
Yace shi mutum ne mai bin doka, yana kuma kiyaye duk wani abin da ka iya jefa shi ko al’umar cikin matsala.
Wannan halin dattako da Adeoye ya nuna ne ya sanya gwamnan jihar karama shi da matsayin anbasadan coronavirus na jihar, ya kuma sanya shi cikin kwamitin da ke yaki da yaduwar cutar a jihar Ekiti.
Gwamna Fayemi ya bayyana halin mutumin a matsayin abin koyi wanda ke abun alfahari ga al’ummar jihar Ekiti inda yace al’ummar jihar ba za su manta dashi ba a al’amarin yaki da cutar coronavirus a fadin jihar.