Wani mutum ya cinna wa kansa wuta a Jos
Da safiyar Alhamis ya banka wa kansa wuta inda ya kone ya sankare
Wani mutum ya banka wa kansa wuta da sanyin safiyar Alhamis 31 ga watan Disamban 2020 a garin Jos, Jihar Filato
Wakilin Aminiya yahalarci wurin da mutumin ya yi wannan danyen aikin a Lambun Peace and Reconciliation Garden, da ke garin Jos.
- An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
- Za mu yaki hauhawar farashin kayan abinci a 2021 —Buhari
- Dalilin rashin tsaro a Gwamnatin Buhari —Kwande
Wani ganau, Misbahu Usman, da ke sana’ar acaba, ya ce, “Babu mutane sosai a lokacin, kan a farga wutar t game jikinsa kuma babu ruwa da za a kashe ta. Ruwan ledan da aka samu bai isa a kashe wutar ba.”
Ya ce abun al’jabin ya faru ne bayan isar mutumin wurin da misalin karfe 7:30 na safe, inda ya bulbula wa kansa fetur ya kyasta wuta ya babbake kansa a kusa da mahadar Maternity Junction a garin na Jos.
Shaidan ya ce daga baya dangi da iyayen wanda ya babbake kansan sun isa wurin inda aka ga mahaifiyarsa na ta kuka.
Ya ce ’yan uwan mamacin sun cika da mamakin abin da ya aikata, inda suka ce ya samu sabani da mahaifinsa da dare ranar Laraba, amma sun daidaita.
Misbahu ya ce dangin mamacin da jami’an ’yan sanda sun dauke gawarsa zuwa asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Aminiya ta ya tuntubi mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato, Ubah Gabriel, amma ya ce zai tuntubi ofishin Rundunar da ke yankin sannan ya waiwayi wakilin namu.