Wani mutum ya kona gidansa saboda kuda

A rahoton da sashen Hausa na jaridar BBC ya wallafa, ya ruwaito wani mutum da tsautsayi ya sanya ya kone wani sashe na gidansa a Faransa a yayin da yake kokarin kashe kuda. Lamarin ya auku ne ranar Juma’a a yayin da dattijon wanda ya haura shekara 80 a duniya ke shirin fara cin abincin […]

Wani mutum ya kona gidansa saboda kuda

A rahoton da sashen Hausa na jaridar BBC ya wallafa, ya ruwaito wani mutum da tsautsayi ya sanya ya kone wani sashe na gidansa a Faransa a yayin da yake kokarin kashe kuda.

Lamarin ya auku ne ranar Juma’a a yayin da dattijon wanda ya haura shekara 80 a duniya ke shirin fara cin abincin dare, sai kawai ya ji wani kuda yana yi masa kai-kawo a kunne.

Ana haka ne dattijon a fusace ya dauki wata ragar kashe kwari mai amfani da lantarki ya fara kai wa kudan duka, ashe tukunyar gas din gidan na yoyo ba tare da ya sani ba.

A sakamakon haka ne aka yi mummunar haduwa tsakanin lantarkin da iskar gas din, lamarin da ya haddasa fashewa wadda ta tarwatsa dakin girkin da kuma wani sashe na gidan da ke kauyen Dordogne a Arewa maso Gabashin garin Bordeaux.

A yayin da mutumin ya tsallake rijiya da baya da kuna maras yawa a jikinsa, a yanzu haka ya koma wani sansani da zama yayin da iyalansa ke gyaran gidan.

NAJERIYA A YAU: Yadda jiragen soji suka kashe fararen a karo na biyu a wata guda

Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa

Aikin titin tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar