Wani mutum ya rasu wajen ciro wayarsa a tsohuwar rijiya a Kano

Hukumar ta tabbatar da rasuwarsa sakamakon zafi da rashin iska.

Wani mutum ya rasu wajen ciro wayarsa a tsohuwar rijiya a Kano

Wani mutum mai shekaru 45, Yusuf Usman, ya rasu a ƙauyen Kwa, da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, yayin ƙoƙarin ɗauko wayarsa da ta faɗa tsohuwar rijiya.

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ta ce ta samu kiran gaggawa ne da misalin ƙarfe 11:13 na safiyar ranar Laraba, inda ta tura tawagar ceto zuwa wajen nan take.

Da isarsu, tawagar ta gano mutumin a cikin rijiyar wadda aka mayar da ita wajen zubar shara.

An ciro shi a sume, amma daga baya aka tabbatar ya rasu.

Rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne sakamakon ƙarancin iska da tsananin zafi a cikin rijiyar.

Hukumar ta ce an miƙa gawarsa ga Hakimin ƙauyen Kwa, Alhaji Muktar.

Daraktan hukumar kashe gobara, Alhaji Sani Anas, ya shawarci jama’a da su riƙa rufe rijiyoyi yadda ya kamata tare da cike waɗanda aka daina amfani da su domin kaucewa irin wannan iftila’i.

Ya kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su ƙara kula da tsaron muhallinsu domin kare rayuka.