Wani mutum ya rataye kansa a Kano

Mun wayi gari da ganin mutumin a jikin reshen bishiyar wuyansa rataye da igiyar dinkin buhu.

Wani mutum ya rataye kansa a Kano

Rataye kai

Ana fargabar cewa wani mutum ya rataye kansa a Unguwar Gaidar Makada da ke Karamar Hukumar Kumbutso a Jihar Kano.

Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito cewa, mazauna sun yi kicibus da mutumin mai shekaru 55 a duniya yana reto a jikin wata birshiryar darbejiya da Asubahin ranar Laraba.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana  cewa “Mun wayi gari da ganin mutumin sanye da kaya ruwan Madara a jikin reshen bishiyar wuyansa rataye da igiyar dinkin buhu [kirtani] sai kuma karin wata wayar cajin waya da ake zargin ya yi amfani da su wajen rataye kansa.”

Manema labarai sun yi kokarin jin ta bakin Dagacin yankin ’Yan Kusa a Karamar Hukumar Kumbotson, Malam Bala Isa, sai dai ya ce zuwa yanzu suna Asibiti don haka sai dai nan gaba zai yi bayani.

Kazalika, Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, sai dai bai amsa kiran wayarsa ba.