Wani mutum ya rataye kansa saboda zargin matarsa da cin amanar aure
Matar tana kwanciya da abokan mijinta saboda ya gaza sauke nauyinsa.
Wani mutum mai kimanin shekaru 38 a duniya, Gabriel Iliya Magaji, ya kashe kansa ta hanyar rataya a unguwar Masaka da ke Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.
Bayanai na cewa ana zargin mutumin ya yi wannan aika-aikar ce a dalilin zargin matarsa da cin amanar aure.
- Direba ya kashe ɗan sanda a Ekiti
- An ba da belin masu zanga-zangar tsadar rayuwa kan naira miliyan 10
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Nansel Rahman, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Litinin ne suka samu rahoton cewa an yi kicibus da gawar mutumin rataye a ɗaya daga cikin azuzuwan wata makaranta da ke Masaka.
Kakakin ’yan sandan ya ce bayan samun rahoton ne aka tura tawagar jami’ai makarantar Crystal School Masaka, inda aka garzaya da shi Babban Asibitin Mararraba, kuma likitoci suka tabbatar da cewa ya cika.
DSP Rahman wanda ya ce babu tabbaci kan ko mutumin ya rataye kansa ne a dalilin zargin matarsa da cin amanar aure, ya tabbatar da cewa suna ci gaba da gudanar da bincike domin bankaɗo musabbabin mutuwarsa.
Sai dai wani saƙo da Aminiya ta yi arba da shi a shafin Facebook, ya bayyana cewa “wani mutum mai kimanin shekaru 38 ya rataye kansa a unguwar Masaka ta Jihar Nasarawa bayan ya gano cewa matarsa tana kwanciya da abokansa domin su ba ta kuɗi.
“Sai dai bayan mutumin ya tunkari matar da batun ne ta shaida masa cewa tana aikata hakan ne saboda shi ya gaza sauke nauyin ɗawainiya da su musamman a ɓangaren abinci.
“Matar ta bayyana cewa tana kwanciya da abokan mijinta domin tana samu kuɗin da take siya musu kayan abinci wanda ita da ’ya’yansu uku da mijin ke ci,” a cewar saƙon.