Wani mutum ya sayar da ’yarsa kan miliyan 1.5 a Bauchi

Mutumin ya yi ƙaryar zai kai yarinyar wajen ‘yar uwarsa da ke zaune a garin Bauchi.

Wani mutum ya sayar da ’yarsa kan miliyan 1.5 a Bauchi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wani mutum da ake zargi da yunƙurin sayar da ’yar cikinsa mai shekara biyar a duniya kan kuɗin Naira miliyan 1.5.

Wanda ake zargin mai suna Yusuf Umar mai shekara 49, ya bayyana cewar yana aiki da ƙaramar hukumar Warji ne.

A cewar rahoton ’yan sandan, Umar, ya riga ya shirya miƙa yarinyar ga wani mutum, sai dai ya yi rashin sa’a wanda zaj sayi yarinyar jami’in ɗan sanda ne da ke aiki a sirri.

“A ranar 26 ga watan Mayu, 2024, wanda ake tuhuma ya ɗauki yarinyar ’yar shekara biyar daga wajen mahaifiyarta a ƙaramar hukumar Warji kan cewar zai kai ta wajen ’yar uwarsa da ke garin Bauchi.

“Mahaifiyar ba ta da masaniyar cewar ya shirya miƙa yarinyar ga waniutum, ba tare da sanin cewa shi jami’in ’yan sanda ne ba,” in ji Kwamishinan ’yan sandan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani otal da ke Bauchi.

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa

Gwamnati ta ba da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suke Haddasa Turmutsutsu A Najeriya