Wani mutum ya shafe shekara 54 bai yi aski ba

Gashin wani mutum mai suna Ake Yizheng  mai shekara 77 dan kasar China ya janyo muhawara ga masu shiga kafafen sadarwar zamani, inda suke kiransa ya nem lambar karramawa ta duniya “Guinness Record.” Ake ya nuna hotonsa ne da ke nuna ya bar gashin kansa ya kai tsawon mita 5.5, zagaye da kansa kamar rawani, […]

Wani mutum ya shafe shekara 54 bai yi aski ba

Ana gyara wa Ake Yizheng gashinsa a shagon aski

Gashin wani mutum mai suna Ake Yizheng  mai shekara 77 dan kasar China ya janyo muhawara ga masu shiga kafafen sadarwar zamani, inda suke kiransa ya nem lambar karramawa ta duniya “Guinness Record.” Ake ya nuna hotonsa ne da ke nuna ya bar gashin kansa ya kai tsawon mita 5.5, zagaye da kansa kamar rawani, inda ya ce, ya haura shekara 54 bai yi aski ba.

An yi ta yada gashin kan Ake Yizheng a shafukan sada zumunta, bayan ’yar surukarsa ta raka shi shagon aski a Leshan da ke Lardin Sichuan a Kudu maso Yamma na kasar China don a wanke masa gashin kansa.

Yarinyar ta dauki bidiyon yadda ma’aikatan shagon askin suke wanke wa Ake Yizheng gashin kan, inda mutum uku suka zagaye shi suna wanke kan, kuma ya kai su tsawan sa’a uku kafin su kammala.

Hoton bidiyon da yarinya ta watsa a shafukan Intanet, ya janyo hankulan masu bibiyar shafukan sama da miliyan 1.5 a ’yan kwanaki kalilan. Wannan hoton ya sanya jama’a da dama bayyana bukatar Ake Yizheng ya nemi hanyar da zai iya samun lambar karramawa ta duniya ‘Guinness Record’, amma a cewar Ake, barin tsawon gashin kan bai da wata alaka wajen fallasa abin da yake da ra’ayi a duniya.

A lokacin da Ake Yizheng yake shekara 23 ya fahimci cewa, barin gashin kansa ya yi tsawo zai kara masa lafiya da iyalansa, don haka tun wancan lokacin bai aske  gashin kansa ba.

Kwanaki ’yar Ake ta bayyana a takarda cewa, a karshen 1970, wani mutum ya sayi gashin kan Ake a kan kudin China Yuan 3,800 wanda ya yi daidai da Naira dubu 205 da 200, amma ya ki amincewa. Ya ce, lafiyarsa da ta iyalansa ta fi masa muhimmanci fiye da kudin da za a ba shi. Ake, ya ce ba zai ji dadin rabuwarsa ba in ba gashin da ya dade yana lura da shi na tsawon lokaci. Saboda ya saba ajiye gashi har kai ga bai askewa.

’Yar Ake ta ce, “Ake yana jin dadin barin gashin kansa. Barin gashin kan Ake bai damunsa.” Ake yana zuwa shagon aski akalla sau biyu a wata ana wanke masa kan, ana gyarawa kuma kamar mutum uku ne ke taruwa su wanke gashin, kuma wanke kan na kaiwa tsawon sa’a uku kafin su kammala.

A cikin masu bayyana ra’ayinsu game da tsawon gashin Ake, wadansu sun bukace shi da ya aske gashin kasancewar tsawon gashin da ya kai mita 5.5.