Wani mutum ya shiga layin zave tun ranar Laraba a Jos domin Buhari

Tun a ranar Laraba ce wani matum mai suna Abubakar Shettima mazaunin Unguwar Duala da ke Dogon Dutse a Qaramar Hukumar Jos ta Arewa ya xebi inasa-inasa ya shiga layin zave domin sake kaxa wa Shugaba Buhari quri’a. Abubakar mai shekara 59 a duniya ya ce ya yi saurin zuwa layin zaven ne domin yana […]

Wani mutum ya shiga layin zave tun ranar Laraba a Jos domin Buhari

Tun a ranar Laraba ce wani matum mai suna Abubakar Shettima mazaunin Unguwar Duala da ke Dogon Dutse a Qaramar Hukumar Jos ta Arewa ya xebi inasa-inasa ya shiga layin zave domin sake kaxa wa Shugaba Buhari quri’a.

Abubakar mai shekara 59 a duniya ya ce ya yi saurin zuwa layin zaven ne domin yana so ya kasance mutum na farko da ya kaxa wa Buhari quri’a a zaven gobe, wanda a cewarsa yake so ya zama tukuici ga Shugaban Qasar bisa taimakonsa da ya yi wajen qwato masa ’yanci bayan an zarge shi da kasancewa xan Boko Haram a shekarar 2015.

“Yanzu haka na tura matata Jihar Borno da safiyar yau (Alhamis) domin ta kaxa quri’a, sannan kuma ina da ’ya’ya uku waxanda dukkansu sun isa yin zave. Biyu daga cikinsu za su zavi Buhari gobe Asabar a nan Jos, xaya kuma ta yi aure tana Maiduguri, wannan kuma sai yadda mijinta ya so.”
Wakiliyarmu ta samu Abubakar zaune a kan sallaya riqe da Qur’ani a wata rumfa da aka liqa sunayen masu kaxa quri’a na wannan akwatin, sannan kuma katin zavensa na dindindin yana aljihunsa.

Abubakar dai xan asalin Jihar Borno ne, inda ya ce shi da wasu xaruruwan mutane an tava kama su ba gaira, ba dalili wai ana zargin cewa su ’yan Boko Haram ne a shekarar 2015.
“A Tashar Motar Bauchi na Jos aka kama ni tare da wasu mutane aka kai mu Jihar Bauchi, daga can aka kai mu Yobe, sannan aka mayar da mu Borno inda aka kulle mu na watanni. Amma bayan Shugaba Buhari ya lashe zave, sai ya ziyarci inda aka kulle mu, da ya ga halin da muke ciki, sai ya bayar da umarnin cewa a rage yadda muke a cakuxe, a sanya mutum 200 a kowane xaki kafin a kammala bincike.”
Malam Abubakar ya qara da cewa bayan an kammala binciken, sai aka gane cewa ba su da laifin komai, “kafin a sake mu sai da Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya ba mu haquri, sannan ya ba mu Naira dubu goma-goma domin mu koma gida.

“Don haka ne domin tukuici ga Shugaba Buhari wanda ba don shi ba, da wataqila ba a sake mu ba, nake addu’ar Allah Ya sa ya ci gaba da mulki saboda talakawa suna tare da shi.”