Wani mutum ya yi kwanaki ba tare da fuska ba

Mutum na farko a duniya da aka yi wa dashen fuska har sau biyu watanni uku ya rayu tsawon kwanaki ba tare da fuska ba. A bara aka cire wa Jérôme Hamon fuskar farko da aka dasa masa bayan da alamu suka nuna jikinsa ba zai karba fuskar ba sakamakon shan wani maganin kashe kwayoyin […]

Wani mutum ya yi kwanaki ba tare da fuska ba

Mutum na farko a duniya da aka yi wa dashen fuska har sau biyu watanni uku ya rayu tsawon kwanaki ba tare da fuska ba.

A bara aka cire wa Jérôme Hamon fuskar farko da aka dasa masa bayan da alamu suka nuna jikinsa ba zai karba fuskar ba sakamakon shan wani maganin kashe kwayoyin cuta da ya yi na mura kamar yadda BBC ta ruwaito.

Mutumin dan shekara 43 ya kasance a wani asibiti a Paris ba tare da fuska a jikinsa ba har tsawon wata biyu, a lokacin ana neman wanda zai bayar da gudunmuwar fuska.

Ya ce da farko jikinsa ya karbi fuskar farko, yanzu ma haka, fuskar da aka sanya masa jikin nasa ya karbeta.

Mista Hamon na fama ne da wata larura mai haddasa kulayen dake bata fuska wacce ake kira neurofibromatosis type 1.

Dashen da aka yi masa na farko a 2010 ya yi nasara, amma a 2015 mura ta kama shi aka kuma bashi maganin kashe kwayoyin cuta (wato antibiotics). 

Sai dai maganin bai dace da magungunan da ake ba shi ba, don haka kwayoyin halittar jikinsa su ka ki karbar dashen da aka yi masa.

A nan ne aka cire fuskar da aka dasa masan, ya kuma zauna tsawon wasu lokuta kafin a dasa masa wata inda ya kasance a asibiti ba ya ji ba ya gani.

Mista Hamon ya rayu babu fuska a wani daki a asibitin Georges-Pompidou na birnin Paris – inda a lokacin ba ya iya gani, ko magana ko jin sauti har zuwa watan Janairu – lokacin da aka sami wanda ya bayar da fuskarsa ga mai bukata.

A lokacin ne aka dasa masa fuskar bayan da aka yi wani aikin tiyata, domin ka da jikin Mista Hamon ya ki karbar sabuwar fuskar da aka dasa masa, an gudanar da wani aiki na musamman domin tsaftace jinin jikinsa wanda kafofin watsa labarai na Faransa suka lakaba wa sunan “mutum mai fuska uku”. 

Kawo yanzu sabuwar fuskar tasa sumul take, kuma ba ta motsi, kana kasusuwansa da fatar jikinsa ba su gama daidaituwa da juna ba. Amma duk da haka yana ganin za a sami nasara a kan aikin.

“Da ban amince da wannan sabuwar fuskar ba, da ban san yadda zan kasance ba. 

Wannan batu ne na ba mutum alamar da za a gane shi… Amma kawo yanzu aikin ya yi kyau”, kamar yadda ya fadawa kamfanin dillancin labarai na AFP daga asibitin da yake murmurewa.

Farfesa Laurent Lantieri shi ne ya yi aikin dashen fuskar da aka shafe sa’o’i ana yi, kuma shi kwararre ne wajen dashen hannu da fuska.

Ya ce ‘ A yau mun gano cewa aikin dashen fuska rubi biyu abu ne mai yiwuwa’.

Ya ce ya ji dadi game da yadda mara lafiyar ya nuna juriya da karfin hali duk da yanayin da ya shiga, hakan ne ya kara ba shi kwarin gwiwa a kan aikin dashen fuskar.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana