Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu

A halin yanzu yarinyar tana ɗauke da ciki da har ya kai watanni tara.

Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 28, Samuel Alfred bisa zargin yi wa wata agolarsa fyaɗe har ta samu juna biyu.

An cafke mutumin ne tare da wani abokinsa, Ikechukwu Obi mai shekaru 30 kan zargin wannan aika-aikar.

Bayanai sun ce ababen zargin sun kai budurwar mai shekaru 14 wani ɗaki da ke yankin Ojo na jihar ta Legas inda suka raba ta da budurcinta.

Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce mahaifiyar yarinyar mai suna Deborah ce ta kai ƙorafi ofishinsu da ke Okokomaiko.

Hundeyin ya ce za a gurfanar da ababen zargin biyu a gaban kuliya domin su girbi abin da suka shuka.

“A halin yanzu yarinyar tana ɗauke da ciki da har ya kai watanni tara kuma za a miƙa lamarin zuwa kotu,” in ji Hundeyin.

PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun

Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu

An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines

Ko Real Madrid za ta iya lashe Gasar Zakarun Turai bana?