Wani mutum yanke makazutarsa a Borno

Mutumin ya daɓa wa kansa wuƙa har sau uku a ciki, kafin ya yanke mazakutarsa da wuƙar.

Wani mutum yanke makazutarsa a Borno

Wuka

An ceto wani mutum mai shekara 50 ya yi yunƙurin kashe kansa a garin Bama na Jihar Borno.

Lamarin wanda ya afku a yammacin ranar Juma’a a unguwar Hausari, inda al’ummar yankin ne suka kai masa ɗauki.

Shaidu sun ce mutumin ya daɓa wa kansa wuƙa har sau uku a ciki, kafin ya yanke mazakutarsa da wuƙar.

An ce ya aikata hakan ne saboda tsohuwar matarsa, daga garin Konduga, wadda ya yi wa saki uku, ta ƙi komawa gidansa.

’Yan sanda sun jagoranci tawagar ’yan sintiri zuwa wurin, inda suka gano tare da ƙwace wuƙar, sa’annan suka kwashi magidancin zuwa Babban Asibitin Bama, inda yake karɓar magani.

Majiyoyi sun ce an miƙa lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) da ke Maiduguri, domin ci gaba da bincike

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya